Kotun Muslunci ta ɗaure wani matashi mai shekaru 25 a gidan yari tare da yi masa bulala kan laifin satar allon shaidar a kabari a wata maƙabarta a Jihar Kano.
Kotun ta ba da umarnin yanke hukuncin kisa ƙeyar matashin zuwa kurkuku ne bayan da ya amsa laifin sace allunan kabari na ƙarfe guda 15 a makabartar.
Daga nan alkalin kotun, Malam Umar Lawal-Abubakar, ya yanke masa hukuncin daurin wata shida a gidan yari tare da umarnin yi masa bulala 30.
Tun da farko mai gabatar da ƙara Insfekta Abdullahi Wada, ya shaida wa alƙalin cewa a ranar Talata ne aka kai ƙarar matashin a ofishin ’yan sanda da ke unguwar Dala.
- Satar N660m: An tsare shugabannin ƙananan hukumomin Kano 3
- Kamfanin China ya ƙwace jirgin Najeriya na 4 a Kanada
An kai ƙarar matashin ne da cewa ya shiga cikin maƙabarta ya sace allunan kabari shaida na karfe guda akalla 15. (NAN)