✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama shi da kokon kan mutum a makabarta

’Yan sanda sun kama wani mai shekaru 45 da ake zargin matsafi ne dauke kokon kan mutum a garin Abeoluta na Jihar Ogun

’Yan sanda sun kama wani mai shekaru 45 dauke kokon kan dan Adam a Jihar Ogun.

Ana zargin mutumin yana shirin yin tsafi da kokon kan ne a lokacin da ’yan sanda suka kama shi.

Kakakin ’yan sandan jihar Ogun, Omolola Odutola, ta ce jami’an rundunar sun kama wanda ake zargin ne bayan da ya haka wani kabari ya sare kan gawar da ke ciki domin yin tsafi a garin Abeokua.

Odutola ta sanar a ranar Talata cewa rundunar ta fara gudanar da bincike kan lamarin.