Wani mutum da ake zargi da tona makabarta yana cire sassan matattu mai suna Samaila Isah ya shiga hannu a garin Zariya da ke Jihar Kaduna.
Aminiya ta ruwaito cewa wannan shi ne karo na biyu da aka kama mutumin mai shekara 44 wanda ake zargin yana fama da lalurar tabin hankali da ke zaune a unguwar Banzazzau cikin garin Zariya.
- Mun kashe ’yan ta’adda 52 a Borno da Yobe — DHQ
- Ban gamsu da hukuncin kotu kan zaben Bauchi ba, zan ɗaukaka ƙara – Sadique
Bayanai sun ce jama’ar gari ne suka kama shi a Juma’ar da ta gabata a lokacin da ya tono kabarin wata yarinya a makabartar Dambo da ke Karamar Hukumar Zariya.
Wakilinmu ya ruwaito cewa al’ummar da ke yankin sun sanya ido a kan shi saboda kai komo da yake yawanyi a kusa da makabartar inda suka same shi dumu dumu har ya cire likafaninta.
A cewar al’ummar wannañ shi ne karo na biyu da aka same shi da irin wannan laifi, inda a wancan lokacin aka ce wai yana fama ne da lalurar tabin hankali.”
Wata majiyarmu ta ce binciken da aka fara gudanarwa ya nuna cewa akwai inda yake kai sassan jikin mutanen idan ya cire.
Da yake tabbatar da kama wanda ake zargin, mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan Sandan Jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan ya ce suna ci gaba da bincike a kan “wanda ake zargin mai suna Samaila Isah.”