Fitaccen malamin Musuluncin nan, Farfesa Ibrahim Maqari ya ce biyan diyya ga masu garkuwa da mutane haramun ne saboda ya saba da koyarwar Annabi Muhammad (SAW).
Ya ce biyan kudaden diyyar kan karfafi ’yan ta’addan ta hanyar ba su damar ci gaba da mummunan aikin nasu.
- ‘Yan bindiga sun nemi fansar N100m kan Shugaban Karamar Hukumar da suka sace
- An kama ’yan damfara masu kwaikwayon muryar aljanu a Katsina
Farfesa Maqari, wanda kuma shi ne Babban Limamin Masallacin Kasa da ke Abuja ya ce, “Haramun ne a nemi taimako domin tattara kudin fansa.
“An rawaito Hadisi cewa wani mutum ya zo wurin Manzon Allah (SAW) inda ya ce masa wani mutum ya yi yunkurin kwace masa kudi ta karfin tsiya, sai Annabi ya ce kada ya sake a kwace masa kudin.
“Sai mutumin ya tambaya, idan ya yi amfani da karfi fa? Sai Annabi ya ce ka yi fada da shi kai ma. Sai ya ce idan na kashe shi fa, Annabi ya ce Wuta zai shiga. Sai ya ce idan shi kuma ya kashe ni fa? Annabi ya ce Aljanna za ka shiga.
“Kun ga ke nan hakan na nuna cewa ba daidai ba ne a biya kudi domin fansar wanda aka yi garkuwa da shi.
“Matukar ana yin haka, masu garkuwar za su rika tafka mummunar asara; Asarar kudin ciyar da wanda suka sace, harsashin da suka yi amfani da shi wurin kashe shi da kuma asarar lokaci.
“Shi wanda suka kashe din lokacin mutuwarsa ne ya yi kamar yadda Allah Ya rubuta.
“Dukkanmu za mu mutu, ko yanzu ko a nan gaba. Mutuwa a hannun masu garkuwa kuma mutuwar shahada ce Insha Allah.
“Idan ba mu yi amfani da wannan koyarwar ta Musulunci ba, ta yaya za a daina garkuwa da mutane?
“Muddin muka ci gaba da biyan kudade domin kubutar da ’yan uwanmu, to haka za su ci gaba da sayen muggan makamai suna ci gaba da ta’asa, har daga karshe su zo su fi karfin jami’an tsaro,” inji shehin malamin.