Dalibai 3 na wata makarantar firamaren gwamnati da ke garin Kubwa-Abuja sun rasa ransu bayan zargin cin biskit da daya daga cikin daliban makarantar ta raba masu a matsayin murnan bikin ranar haihuwa.
Lamarin wanda ya faru a ranar Talatar da ta gabata, Aminiya ta samu labarin cewa da farko ya ritsa ne da wani dalibin makarantar mai suna Yahaya Garba dan shekara 13 dan aji 4, sai kuma wata daliba mai suna Na’imat Yahaya ’yar shekara 14 da ke aji 5 da kuma dalibi na uku mai suna Moses Sunday dan aji 1 da suka rasu a ranar Laraba bayan an garzaya da namijin zuwa babban asibitin garin, a yayin da macen kuma aka kai ta wani asibiti mai zaman kansa da ke kusa da unguwarsu Kubwa-billage mai suna Daughter of Charity, kamar yadda kanin mahaifin yarinyar ya bayyana.
daya daga cikin iyayen mamatan mai suna Malam Ahmadu Garba Makeri ya ce dansa Yahaya ya dawo gida gabanin lokacin tashi makaranta a ranar ta Talata, inda ya yi korafin rashin jin dadin jiki. Ya ce ya sa yaron ya ci abinci sannan aka ba shi maganin zazzabi da na zafin jiki ya sha ya samu kuzari, sai dai ya ce daga baya yaron ya kama hararwa, inda aka garzaya da shi zuwa babban asibitin garin, inda a can ne kuma aka tabbatar masa da cewa ya rasu.
Shugaban karamar Hukumar Bwari, Mista Musa Dikko wanda ya ziyarci makarantar tare da ayarin da ya wakilci Ministan Abuja Malam Muhammad Musa Bello da sauran shugabannin tsaro, ya sanar da ’yan jarida a cikin harabar makarantar bayan ganawarsu da wasu iyayen yara da kuma malamai cewa, dalbai biyu masu suna Hasiya Haruna da kuma A’isha Isa an garzaya da su zuwa babban asibitin garin, inda ake kulawa da su. Sai dai ya ce daya daga cikin mamatan mai suna Moses dan aji daya, ya rasa ransa ne a sakamakon fada da wasu dalibai biyu kamar yadda ya samu bayani.
A bayanin da ya yi, shugaban ’yan sandan Kubwa (DPO) C.S.P Ayobami Surajudeen, wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce bayan fara gudanar da bincike, an kama mutum 2 dangane da lamarin, a yayin da kuma aka rufe makarantar har zuwa ranar Litinin mai zuwa. daya daga cikin daliban da ke asibiti mai suna Hasiya, ta ce wata ’yar ajinsu ce mai suna Salamatu ta raba masu biskit a cikin aji suka ci.