Shugaban Kiristoci mabiya darikar Katolika shiyya Sakkwato, Bishop Mathew Hassan Kukah, ya bayyana damuwa kan halin tabarbarewar tsaro da Najeriya ta tsinci kanta a ciki.
A hudubarsa ta bikin Easter a ranar Lahadi, Bishop Kukah ya soki Gwamnatin Shugaba Buhari wadda ya ce a wuyanta nauyin tsare rayuka da dukiyoyin al’ummar kasar ya rataya.
- Masoyan Buhari sun mamaye gidan Gwamnatin Najeriya a Landan
- Har yanzu APC ‘hatsin bara’ ce – Ganduje
A hudubar mai taken “Najeriya: Gabanin gushewar daukakarmu”, Bishop Kukah ya ce Najeriya ta zamto tamkar wani dandalin na kisa ganin yadda mayakan Boko Haram da ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke cin karensu babu babbaka.
Babban limamin cocin ya ce, a sanadiyar haka, Najeriya na iya rasa kimarta a wurin masu aikata miyagun laifuka muddin gwamnati ta zuba musu idanu ba tare daukar wani kwakkwaran mataki ba.
“Muna cikin wani mummunan tarnaki mai dimautarwa na yanke kauna tare da janyo damuwa da bakin ciki da wahala.
“Ba mu da wani sako kuma ba mu da masaniya game da yaushe wannan yanayi zai gushe.
“Mutanenmu suna neman kwanciyar hankali da kariya amma takaici da duhu na barazanar sun nutsar da su,” inji shi.
Ya ci gaba da cewa, a daidai lokacin da gwamnati ke kashe makudan kudaden waje sauya tunani da gyara halayyar tubabbun mayakan Boko Haram da ’yan bindiga, mutanen da suka daura damarar ta’addanci na kara kashe dubban mutane da barnaa dukiyoyi da tilasta wa al’umma barin matsugunansu.
Kazalika, Bishop Kukah ya sanya ayar tambaya kan abin da zai sa ’yan kasa su ci gaba da mutunta Gwamnati alhali ita take kula da lafiyar masu kashe su da yi musu illa, su kuma aka bar su da binne danginsu da aka kashe.
Ya kuma ankarar da Shugaba Buhari a kan yadda ya rika cika baki da bugun gaba yayin da ya karbi ragamar jagorancin kasar, inda ya rika bayyana Boko Haram a matsayin karamar wutar da aka bari ta girma.
Ya ce ga shi yanzu a karkashin mulkinsa ana gani fitintunu na tashi a sassa daban-daban na kasar suna kuma neman durkusar da ita.
A karshe, Bishop Kukah ya nemi ’yan kasar da su dage wajen yin addu’o’in samun saukin matsalolin da ake fuskanta a kasar.