Gwamnatin Birtaniya ta dakatar da daukan ma’aikatan lafiya daga Najeriya.
Wannan dai na kunshe ne cikin sabuwar dokar daukan ma’aikatan ketare da Gwamnatin Birtaniyar ta yi wa kwaskwarima da ta wallafa a shafinta na Intanet.
- Boko Haram ta kashe mutum 10 a yankin da ISWAP ta mamaye a Borno
- Ramadan: Yobe ta Ware N103m Don Ciyarwa da Wa’azi
Da wannan dai a yanzu Najeriya ta shiga sahun kasashen duniya da Kungiyar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana a matsayin masu bukatar gaggawa ta fuskar karancin ma’aikatan lafiya da za su jibinci lamarin kiwon lafiyarsu.
A watan Maris ne WHO ta wallafa sunayen kasashen duniya 55 da ke fama da karancin ma’aikatan lafiya ciki har da Najeriya.
Gwamnatin ta Birtaniya ta ce akwai bukatar Najeriya da sauran kasashen da lamarin ya shafa su mayar da hankali wajen bunkasa harkokin kiwon lafiyarsu musamman ta hanyar dakile daukar ma’aikatan lafiyarsu aiki da ake yi a ketare.
A ranar Alhamis ta makon jiya ce Majalisar Wakilai ta amince da kudirin da ke shirin tilasta wa likitoci share shekaru biyar a Najeriya kafin samun izinin zuwa kasashen waje aiki.
Wani dan Majalisar Wakilan na jam’iyyar APC daga Legas, Ganiyu Johnson, ne ya dauki nauyin kudirin da ke neman a yi wa Dokar Likitoci ta 2004 kwaskwarima.
Galibi ’yan majalisar da suka kada kuri’ar baka sun amince da kudirin, sai dai wasunsu sun nemi a yi wa kudirin sakwa-sakwa ta yadda wadanda abin zai shafa za su samu zabin aiki a kasar ko tafiya ketare.
Wannan lamari dai wani sabon abu ne da ka iya kai wa ya zamo sabon rikici a tsakanin Gwamnatin Tarayyar da Kungiyar Likitoci NMA.
Ya zuwa yanzu, akalla likitoci dubu biyu ne ke barin kasar a shekara da sunan ci rani.
Haka kuma, kwarrarun likitocin Najeriya sun yi nisa a kasashen Turai da ’yan uwansu na Gabas ta Tsakiya, inda ke zaman sababbin matattarar likitocin da ke fadin ba dadi cikin kasar a halin yanzu.
To sai dai kuma bayan share tsawo na lokaci tana guna-guni a kuryar daki, tarrayar Najeriyar na neman mafita tare da wata dokar da ta tilasta daukacin likitoci na kasar share shekaru guda biyar suna aiki kafin samun izinin damar yin aiki can a kasashe na waje.
Dokar da ta tsallaka mataki na biyu na zauren majalisar, na da babban burin kawo karshen kaurar da likitoci ke yi zuwa ketare.
Duk da dimbin makarantun aikin likita, har ya zuwa yanzu yawan likitoci cikin kasar bai haura dubu 25 ba a Tarayyar Najeriyar da ke da mutane miliyan 200 da kadan.
Sabuwar dokar ta fara jawo takkadama, inda kungiyar likitoci ta kasar NMA ta ce, a kai ga kasuwa.
Kungiyar NMA dai ta ce, maimakon a dora wa kare laifin kura, kamata ya yi a kalli mai ya janyo maitar tun daga farko.
Kyautata tsarin aiki ko kuma kokari na murde wuyar ’yan cin rani dai, kusan kaso sittin cikin dari na likitoci na kasar a fadar kungiyar kananan likitoci na kasar na neman hanyar fita da nufin inganta rayuwa da makomar likitocin Najeriyar.
Ya zuwa yanzun, likita guda daya ne ke duban marasa lafiya dubu 30 a Kudancin kasar, a yayin da adadin ya kai dubu 45 a Arewacin kasar.