✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Birtaniya ta bukaci Scotland kada ta balle

A shekaranjiya Laraba ne Firaministan Birtaniya ya yi kira ga al’ummar yankin Scotland da kada su balle daga Birtaniya  lokacin taron kanfe a yankin, gabanin…

A shekaranjiya Laraba ne Firaministan Birtaniya ya yi kira ga al’ummar yankin Scotland da kada su balle daga Birtaniya  lokacin taron kanfe a yankin, gabanin gudanar da kuri’ar raba-gardama kan ko yankin zai ci gaba da zama a karkashin Birtaniya, ko kuma a’a.
Firaminista Dabid Cameron da Mista Ed Miliband jagoran jam’iyyar Labour da kuma mataimakin Firaminista Nick Clegg na jam’iyyar Liberal Democrat sun  jagoranci kanfe  din ne a garuruwa daban-daban da ke yankin a wani yunkuri na goyon bayan kasancewar yankin a karkashin Birtaniya, kafin gudanar da kuri’ar ranar Alhamis mai zuwa.
Jagoran gwamnatin yankin Scotland, Aled Salmond ya ce “ba a taba samun shugabanni ne da ba su da gaskiya ba a tarihin Birtaniya  kamar wadanda ake da su yanzu”. Kuma ya sha’alwashin cewa ziyarar ta su za ta kara ba masu goyon bayan ballewar ne kwarin gwiwa. Har ila yau, ya ce zai so a ce firamistan ya tunkare shi ne kai tsare donmin su yi muhawara kan batun.
Hakazalika, a wata makala da aka wallafa a jaridar Daily Mail shekaranjiya, Mista Cameron ya bukaci al’ummar yankin Scotland da su zabi ci gaba da kasancewarsu a karkashin Birtaniya. Inda ya ce: “Kyakkyawar makomar yankin Scotland ya ta’allaka ne akan kasancewarta da Birtaniya, amma fa ta hanyar samun sabbin karfin iko”. Ya kuma ce sabon lalen da za a yi zai taimaka wajen fayyacewa jama’ar yankin zaben abin da ya dace da su a lokacin kada kuri’arsu.
Ya kara da cewa: “Birtaniya wata kasa ce mai dimbin albarka kuma wadda ta bambanta da tsara. Wannan ya sa take da karfin fada a ji. Saboda haka kada duk wani da ke Scotland ya yi shakku kan batun cewa muna mutukar bukatarsu, kuma ba ma so wannan  dangantakar ta kawo rabuwar kasashen”
Yankin Scotland wanda yake da arzikin man fetur da iskar gas dai ya shafe fiye da shekara 300 a karkashin Birtaniya. Kuma akwai akalla masu kada kuri’a fiye da miliyan hudu a yankin da a halin yanzu  za su bayyana ra’ayinsu akan ci gaba da hadakar, ko kuma ballewa don samun ’yancin kai.  Idan masu goyon bayan ballewar suka samu nasara, jam’iyyar Scottish National Party, wadda ita ce ke mulkin yankin, ta ce za ta  bayyana ranar 24 ga watan Maris din shekarar 2016, a matsayin ranar ’yancin kan yankin.