Najeriya ta yi babban rashin mai kishin kasa a makon jiya, inda a ranar Lahadi 25 ga watan Nuwamba 2018, Allah Ya karbi ran Birgediya Abba Kyari bayan gajeruwar rashin lafiya a Abuja. Ya rasu yana da shekara 80, tunawa da shi na da matukar muhimmanci a matsayinsa na tsohon Gwamnan mulkin soja a Jihar Arewa ta Tsakiya wanda a yanzu ta hada da jihohin Katsina da Kaduna.
An haifi Abba Kyari ne a 1938, ya yi makarantar Midil ta Borno da Kwalejin Barewa ta Zariya. A 1959 ya shiga makarantar sojojin Najeriya inda ya fito da mukamin kadet, ya halarci makarantar horar da jami’an sojoji a garin Teshie da ke Accra kasar Ghana daga watan Maris 1959 zuwa watan Satumba 1959.
Kyari ya halarci makarantar horar da sojoji ta Birtaniya ‘British Army’s Mons Officer Cadet School’ a Aldershot daga watan Oktoba na 1959 zuwa watan Maris 1960. Ya taba zama kwamandan inda yake aiki daga nan ya zama jami’in sufuri na sojojin Najeriya ‘Nigerian Army’s 1 Brigade Transport Company’. A watan Yulin 1960 ya samu mukamin Manjo a soja.
An bai wa Manjo Kyari umarnin fara aiki da mukaminsa a bataliya ta 5 ta sojojin Najeriya a watan Satumba 1966 bayan juyin mulkin watan Janairu da Yuli. Ya zama kwamanda ta dakaru ta 1 a Kaduna yayin da ya zama mai mukamin na biyu da ke bayar da umarni na dakarun sojojin Najeriya na kasa.
A lokacin da aka samu barkewar rikici a yankin Arewa wanda ke da alaka da siyasa a wanncn shekarar. Manjo Abba Kyari ya samu nasarori a fannoni daban-daban daga cikin abokan aikinsa yayin da ya zauna a yankin Gabashin Najeriya. Ya kasance mai kishin kasa da son zaman lafiya, wanda ake alfahari da yadda yake gudanar da rayuwarsa a lokacin.
A 1967 lokacin mulkin Janar Yakubu Gowon wanda ya kirkiro jihohi 12 a kasar nan da 6 daga ciki a yankin Arewa ne, sai aka nada Kanar Abba Kyari a matsayin Gwamnan Jihar Arewa ta Tsakiya na farko lokacin mulkin soja. Ya gudanar da mulkin jihar har zuwa lokacin da aka kawar da gwamnatin Gowon a watan Yulin 1975. Ana tunawa da tsarin gina Jihar Kaduna da marigayin ya yi lokacin mulkinsa. An samu sauyi daga tsarin da marigayin ya tsara ne a birnin jihar, bayan faruwar wasu matsaloli da gwamnatin jihar ta gada.
A matsayinsa na jami’in soja mai rike da mukamin ofishin farar hula, Abba Kyari ya gudanar da mulkinsa kamar lokacin mulkin soja. Yana daya daga cikin wadanda suka bayar da kwarin gwiwar dawo da mulkin farar hula a kasar nan, wandaa karshe Janar Murtala da Obasanjo suka samar da Jamhuriya ta Biyu a watan Oktoba 1979. Bayan yin ritayarsa ya kasance cikin masu kokarin hada kan kasar nan don zama dunkulalliyar kasa. A kokarin hakan ne ya jagoranci ayarin wakilan ’yan Arewa zuwa taron dokokin kasa a 1994, kuma an zabe shi a matayin shugaban kwamitin tsaro na taron.
Abba Kyari, ya kasance mai saurin daukar matakan gyara a duk inda ya tsinci kansa harda kamfanonin da ya yi aiki. Ya rike mukamin Darakta a bankin First Bank na Najeriya da Kamfanin Inshora na Standard Alliance da Bankin Kasuwanci na Merchant Bank of Commerce. Kyari ya taba zama Shugaban KamfaninFulawa na Gamah Flour Mills da kamfanin gine-gine na Alif Engineering and Construction, kafin daga bisani ya yi ritaya, ya zauna shiru a a Maiduguri babban birnin Jihar Borno lokacin da babu rikici.
A sakon ta’aziyyar Shugaba Muhammadu Buhari ga gwamnati da jama’ar jihohin Kaduna da Katsina da Borno ya ce, “Mun yi jimamin rasuwar Janar Abba Kyari babban jami’in soja da muke girmamawa.” Shugaba Buhari ya roki Allah Ya gafarta masa da bai wa iyalansa hakurin rashin. Marigayin ya rasu ya bar ’ya’ya tara ciki akwai Abubakar Kyari, Sanatan da ke wakiltar mazabar Borno ta Arewa a yanzu. Ya rasu yana jikoki da ’ya’yan jikoki da dama, an yi masa jana’iza a Abuja kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Allah Ya jikansa da rahama, amin.