✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Binuwai na shirin mika kwalejinta ga Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Jihar Binuwai ta bayyana shirinta na mika kwalejin koyon sana’o’i ta garin Igbokolo da ke karamar hukumar Okpokwu na jihar ga gwamnatin tarayya. Gwamnan…

Gwamnatin Jihar Binuwai ta bayyana shirinta na mika kwalejin koyon sana’o’i ta garin Igbokolo da ke karamar hukumar Okpokwu na jihar ga gwamnatin tarayya.
Gwamnan jihar Samuel Ortom ya shelanta haka ne a bikin hadin gwiwa na yaye daliban kwalejin na shekarar 2006 zuwa shekarar 2016.
Ortom ya ce gwamnatinsa za ta kafa kwamitin da zai gudanar da aikin mika makarantar ga Gwamnatin Tarayya.