✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bindigogi araha a kasuwa

A wani bincike da kungiyar ‘Arewa House Centre for Historical Documentation and Research’ ta gudanar a kwanan nan, ta koka da abin da ta gano,…

A wani bincike da kungiyar ‘Arewa House Centre for Historical Documentation and Research’ ta gudanar a kwanan nan, ta koka da abin da ta gano, na yadda ake tallatawa da sayar da bindigogi da sauran makamai a kasuwannin da ke kan iyakokin kasar nan ta bangaren Arewa. Binciken ya gano cewa, ana sayar da bindiga, kirar AK47 da alburusai 20 a kan Naira dubu 10 kacal. Wannan abin takaici ne kuma al’amari ne da ya kamata ya jefa kowa cikin tsoro. Wannan kuma ya kara tabbatar mana da cewa hukumomin da ke da alhakin kula da al’amarin ba su yin aikinsu yadda ya dace.
Wasu na ganin cewa ba wani abu ne ya haifar da hauhawar makamai a kasar nan ba, sai yadda sojoji suka dade cikin al’amuran mulkinmu, kamar kuma yadda al’adar nan ta tashin hankali ta yi tasiri a cikin al’ummarmu. Wani abin lura shi ne, idan har za a alakanta batun ga mulkin soja, to amma bukatarsu ta zarce ta kananan barayi da ’yan fashi. A yanzu kabilun da ba sa jituwa da wasu, sukan yi amfani da makaman domin daukar fansa ko kuma ramuwar gayya, koda kuwa an dade da sasanta su ta hanyar tattaunawa. A wannan zamani da muke ciki, a sanadiyyar fadace-fadacen kabilanci, ana tafka asara mai yawa ta rayuka da dukiya da kadarori. Yadda ake samun bindigogi da sauran makamai cikin sauki, ya taimaka wajen haddasa fadace-fadace tsakanin manoma da makiyaya da sauran ire-irensu a kusan dukkan sassan kasar nan.
A yanzu, babu wani tashin hankali da ya yi kaurin suna kuma yake nuna yadda makamai suka yi yawa a kasar nan kamar na yankin Neja-Delta da kuma na Boko Haram. A yankin Neja-Delta, mallakar makamai ya zama ruwan dare, inda al’amarin ya zama abin tsoro da barazana, yankin ya zama wani bagire na yaki. Nan za ka ga kungiyoyin barayi da ’yan ta’adda suna cin karensu ba babbaka, har ma suna neman dakile ko gurbata tafiyar da al’amuran mulki a yankin. ’Yan bindiga a yankin suna kawo wa harkar tattalin arziki cikas da tarnaki, suna lalata bututun mai, suna yin garkuwa da mutane don amsar kudin fansa, kamar kuma yadda suke satar danyen mai. Haka kuma, manyan barayin mai na duniya, suna amfani da su wajen satar danyen man, suna fitar da shi daga kasar nan zuwa kasashen waje. Babu shakka, lokaci ya yi da za a zauna a nemo mafi dacewar yadda za a kawo karshen wannan aika-aika. Wannan kuwa kalubale ne ga hukumomin da ke kula da afuwar da aka yi wa masu tada kayar baya na Neja-Delta, domin kawo karshen ta’annatin.
Babu mamaki idan muka ce al’amarin Boko Haram ya fara sassautawa, amma kuma ba za a mance da mummunan rashin da ake yi ba na rayuka da na dukiya. Don haka, a bayyana take, illar da yawan makamai da ke hannun mutane suke haifarwa da kuma barazanar da suke kawo wa al’umma ta fuskar zaman lafiya a Najeriya.
Domin dakile balahirar, kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Afrika Ta Yamma ta kafa kwamitin da zai duba yiwowar mangace matsalar, sai dai daga dukkan alamu, ta’azzarar da yawan makaman suka yi a hannun jama’a, ya sa kwamitin ke fuskantar babban kalubale. Bisa ga haka, ya dace kasashen da ke cikin kungiyar su tashi tsaye, su karfafa hukumomin tsaro kamar Hukumar Kwastan da ta Shige-Da-Fice da kuma Hukumar ’Yan Sanda, domin su fuskanci magance matsalar da gaske.
Haka kuma, kasashen da ke cikin yankin kungiyar ta ECOWAS, ya dace su kafa cibiyoyin da za su tarbi aikin dakile shiga da makamai ba bisa ka’ida ba, sannan a tsaurara dokar mallakarsu, kamar kuma yadda za a tanadi hukunci mai tsauri ga wanda duk aka kama da karya irin wannan doka ko aikata laifin.