Da yammacin ranar Alhamis ne a ka fara yaɗa labarin cewa an kai mummunan hari a Babban Bankin Najeriya (CBN).
Wannan labari ya karaɗe kafofin sada zumunta musamman dandalin Facebook.
Jita-jitar ta yaɗu cewa an kai harin ƙunar baƙin wake a babban bankin Najeriya inda ta yi mummunar ɓarna.
Har wa yau, jita-jitar ta yaɗu ne a tsakanin wasu shafuka da suke yaɗa abubuwansu da harshen Hausa waɗanda ba gidajen jaridu ba na.
Sai dai binciken da Aminiya ya tabbatar da cewa hotunan da ake yaɗawa na ƙarya ne waɗanda aka haɗa da basirar na’ura (AI).