A bukukuwan Sallah da ake shirin farawa a ranar Litinin a Jihar Gombe, Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Civil Defence (NSCDC) ta jibge dakarunta 614 a wurare daban-daban a Jihar.
Kwamandan hukumar a Jihar, Waziri Babagoni Goni ne, ya bayyana hakan ga manema labarai, inda ya ce tuni hukumar ta tura jami’ai 614 don sanya ido da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a lokacin shagulgulan Sallah.
- Abin da ’yan Najeriya ke cewa kan rashin ganin wata
- Budaddiyar wasika zuwa ga ’yan bindigar Arewa maso Yamma
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamandan hukumar ya aike wa manema labarai ta hannun Kakakin hukumar, DSC Buhari Sa’ad.
A cewarsa tura jami’an yana nuni ne da cewa za su yi aiki a wuraren don samar da tsaro bisa umarnin da babban Kwamandan hukumar na kasa Abubakar Ahmed Audi, ya umarce su.
Ya kuma ce an tura jami’an ne a masallatai, wuraren shakatawa, tashohin mota, kasuwanni da sauran wuraren taron jama’a.
Waziri, ya taya daukacin al’ummar musulman duniya murnar zagayowar karamar sallah da fatan za a yi bikin sallah lafiya.
Sannan ya hori jami’an hukumar da su kasance masu yin aiki bisa tsarin doka su kuma kare hakkin dan adam.