Gwamnatin jihar Neja ta sanar da hana kilisa da hawan Sallah yayin bukukuwan Karamar Sallar bana
Sakataren Gwamnatin Jihar, Ahmed Ibrahim Matane wanda ya bayyana hakan ya ce daukar matakin ya biyo bayan karbar korafe-korafen da aka samu kan zargin wasu na kokarin fakewa da yanayin wajen tayar da zaune tsaye.
- Fasinjoji 14 sun kone kurmus a hatsarin motar hanyar Legas
- Ba za mu goyi bayan juyin mulki ba – Afenifere
Ya yi kira ga jama’ar jihar da su kiyaye dokar, inda ya ce ba za su lamunci dukkan wanda ya yi kokarin karyata ba.
Daga nan sai ya gargadi masu dawakan da su gargadi yaransu, yana mai cewa duk wanda aka kama zai dandana kudarsa ta hanyar tsare shi kuma za a kwace dokin nasa.
Bugu da kari, ya ce gwamnatin ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen gurfanar da duk masu kunnen kashi a gaban kuliya.
Ya ce, “Gwamnati mai ci ba za ta zauna ta nade hannunta ta bar bata-gari su ci gaba da cin karensu ba babbaka ba.
“Ba za mu kyale kowacce irin barazanar tsaro ba a kowanne irin yanayi ba tare da daukar mataki ba,” inji shi.
Ya kuma ba al’ummar jihar tabbacin cewa za su magance kowanne irin kalubalen tsaro a jihar nan ba da jimawa ba, tare da kiransu da su ci gaba da addu’a don ganin karshen matsalar tsaron da ta ki ci taki cinyewa a jihar.