Hukumar dake kula da sayar da man Fetur ta Najeriya DPR ta ce, ta adana sama da litar man fetur miliyan 25 a wajen ajiyarta don tabbatar samar da wadataccen man fetur a lokacin bikin karshen shekara.
A yayin da yake yi wa manema labarai jawabi Kwantirolan Hukumar DPR na shiyyar Kaduna Isa Tafida, ya ce, an ajiye man fetur din ne saboda kaucewa karancin man fetur da aka sabayi a duk karshen shekara.