Hukumar Gudanarwar Kamfanin Media Trust Limited, Abuja da ke buga jaridun Daily Trust da Aminiya, ta tsayar da ranar 5 ga watan Yunin bana, a matsayin ranar da za a gudanar da gagarumin bikin mika kyaututtuka ga zakarun da suka lashe gasar rubutun gajerun labarai na Aminiya.
Gasar wacce ta gudana a bara, ta samu tsaiko ne sakamakon matsalolin da cutar COVID-19 ta haifar, wanda dalili ke nan aka jinkirta bikin mika kyaututtuka ga zakarun da suka nuna bajinta, sai wannan lokaci.
- Mutumin da ya nemi kashe Limamin Masallacin Harami ya yi ikirarin shi ne Mahadi
- An kama mahaukaciya da bindigogi a Legas
- Sirrin lashe gasar rubutun gajerun labarai
Shugaban Kwamitin Gasar, Farfesa Ibrahim Malumfashi, ya ce zakaru uku ne suka yi wa dimbin wadanda suka fafata a gasar zarra, inda a ranar bikin za a fitar zakara daga cikinsu.
Mutum uku sun hada da Mubarak Idris Abubakar, wanda ya shiga gasar da labarinsa mai taken ‘Tufka Da Warwara.’ Sai Ubaida Usman, wanda ta yi nasara da labarinta mai taken ‘Ranar Kin Dillanci. Akwai kuma Rufaida Umar Ibrahim, wacce ta yi nasara da labarinta mai taken ‘Dimokuradiyar Talaka.’
Haka kuma, akwai marubuta 12 da suka ciri tuta a gasar, wadanda su ma za karrama su a ranar bikin, wanda zai gudana a Otel 17, da ke Lamba 6, Titin Tafawa Balewa/Lafiya, Kaduna da misalin karfe bakwai na dare.
Wannan gasa, wacce AMINIYA-TRUST da GANDUN KALMOMI da OPEN ARTS suka gudanar a madadin Kamfanin Media Trust Nig. LTD, za a ci gaba da gudanar da ita kowace shekara idan Allah Ya yarda, da nufin bunkasa Adabin Hausa.