✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bikin Bianou a garin Agadas

An shafe mako guda ana bikin sallar Bianouè a birnin Agadas da ke Jamhuriyar Nijar. Wannan biki na al’ada ne da ake danganta shi da…

Abzinawa sun fito bikin sallar ‘Bianou’An shafe mako guda ana bikin sallar Bianouè a birnin Agadas da ke Jamhuriyar Nijar. Wannan biki na al’ada ne da ake danganta shi da hijirar Manzon Allah (SAW) wadda ya yi daga birnin Makka zuwa Madina, don haka za ka ga kowa a bikin Bianou rike da ganyen dabino da gangar mandiri da ake kira ‘akasamù’.
Wadanda suka shirya bikin sun bayyana wa manema labarai cewa wannan rana ce ta kure adaka “Ranar bikin bianou; ranar kure adaka ce ga daukacin al’ummar Abzin, inda kowane dan gari zai ci ado, ya rike mandirinsa na ‘akasamu’ yana bugawa, Don haka a iya cewa kusan kowane dan Abzin yakan yi wa wannan rana babban shiri har ta kai ga ana gasar ado tsakanin Abzinawan Gabas da na Yamma. A bana Abzinawan Gabas suka cinye domin sun caba ado, sun kada mandirinsu sun kuma kwashi rawa, saboda takaicin wannan kaye da ‘yan Yamma suka sha sai al’amarin ya kai ga fada. Da kyar aka shawo kan al’amarin.”
Da aka tambayi Attka Tambari shugaban matasan yamma kuma shugaban bikin sallar Bianou na birnin Agadas cewa wannan bikin addini ne ko al’ada sai ya ce, “Bikin Bianou al’ada ce wadda aka gada iyaye da kakanni, inda Abzinawan Agadas ke daukar 10 ga Muharram don tunawa da hijirar Manzon Allah SAW daga birnin Makka zuwa Madina, don haka suke tafiya daji su kwana, ta yadda idan Buzu ya cika namiji; zai tafi ya bar iyalansa, ya kwana a daji, inda ake jiran ko-ta-kwana, daga bisani a fito, kowa ya sha nadi; ta yadda ba a iya gane kowane, daga nan a fara kade-kade da raye-raye har zuwa gidan Sarki, inda za a cashi rawa ‘yan Gabas da Yamma su hadu kowa ya nuna bajintarsa¨
Wani yaro yake shirin fita bikin Bianou a AgadasBayan an kammala sai Sarki ya gabatar da jawabinsa na godiya da marhaba, ya kuma yi salla.
Duk da cewa an yi sulhu tsakanin ‘yan Gabas da Yamma, kimanin shekara 30 ba a yi fada ba; amma bana sai da aka yi artabu, saboda ranar jajibirin Bianou rawa da kidan ‘yan Gabas ya fi burge kowa; su kuwa ‘yan Yamma suka kasa jurewa, don haka sai fada ya barke a cewar wani wanda al’amarin ya auku a gabansa.
Ranar Larabar makon jiya ana gudanar da sallar Bianou lafiya, an kai gaisuwa gaban Mai martaba Sarkin Abzin, Alhaji Omar Ibrahim Omar kuma fadawansa sun yi hawa, sarki ya yi addu’o’i tare da malamansa inda aka kyale al’ummar gari  suka cashe.
Sardaunan Abzin, Dokta Abdulkadir Labaran Koguna, ya gana da Aminiya, inda ya bayyyana cewa wannan bikin mutanen Abzin sun saba gudanar da shi kimanin shekara 829 da suka gabata, sannan ya yi nuni da alakar hijirar da murnar bikinta; kan cewa Shehu Usman dan Fodiyo ma malamin Sheikh Jibrilla Bn Umar ya umarce shi da ya je kasar Hausa ya yi wa’azi. A cewarsa; wannan al’amari shi ke nuni da alakar Najeriya da kasar Nijar, kuma hijira ce ta haifar da haka, sannan ya ambato wadansu mashahuran mutane, wadanda suka hada da Malam Haido da Sheikh Malam Atamma, wadanda suka yi shahara a Najeriya da cewa duk ‘yan Agadas ne.
Yayin wannan bikin ko ina aka zagaya a birnin Agadas za a ga daukacin al’umma na cike da farin ciki. Wannan biki dai ya yi armashi a bana.
‘Yan Najeriya da dama sun halarci bikin Bianou a bana, don haka Aminiya ta gana da mutanen da suka hada da Kwamared Garzalli, tsohon sakataren kungiyar Ma’aikata ta Jihar Kano da Alhaji Auwalu Babba dandago, tsohon Kansila a karamar Hukumar Gwale ta Jihar Kano da Ahmad Sadi Bello, tsohon Shugaban Majalisar Kansiloli ta Gwale da Dokta Salihu Abdullahi bagwai, Shugaban Tsangayar Kimiyyar Sarrafa Sinadarai a Kwalejin Ilimi ta Bichi, sai kuma Rabi’u Suleiman Bichi, Malami a Kwalejin Ilimi ta Bichi da Mahlud Alkasim da Malam Usman Musa Gabari sun yaba da yadda aka gudanar da bikin Bianou a bana, inda suka bayyana cewa hakika bikin ya kayatar da su.