✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bidiyon tsiraici: Dan hadimin Tambuwal ya gurfana a kotu

Ana kuma zargin su da sayar da littafin batsa da zubar da ciki da dangoginsu

Kotun Majistare ta Jihar Sakkwato ta gurfanar da wasu matasa uku bisa zargin yada bidiyon tsiraicin wata budurwa a shafukan sa da zumunta.

An gurfanar da dan Mashawarci na Musamman ga Gwamna Aminu Tambuwal ka Kyautata Rayuwa, Umar Abubakar da abokansa biyu ne bisa zargin zubar da ciki da kuma sayar da littafin batsa da dangoginsu.

Dan sanda mai shigar da kara, ASP Samuel Sule  ya shaida wa kotun cewa abin da wadana ake tuhuma suka aikata sun kuma hada da alfasha, zubar da ciki, da kuma bugawa da sayar littafin batsa don cin mutunci.

Hakan, a cewarsa laifuka ne karkashin sashe na 60(2), 377, 262, 48, 171, 173 da 379 na Kundin Laifukan Jihar Sakkwato na 2019.

Bayan sauraron bayanan, alkalin kotun, Mai Shari’a Shu’aibu Ahmad ya ce kwararan hujjoji sun tabbatar da zargin, a kan matasan uku, amma ya sallami mutum na hudu saboda rashin alakarsa da wani laifi a shari’ar.

Kotun ta sake fitar da laifukan da ake tuhumar su da aikatawa da suka hada da badala, zubar da ciki, da fitsara da kuma sayar a littafin batsa wadanda laifuka ne karkashin sashe na 48, 171 da 173 na Kundin Laifuna na Jihar Sakkawato.

Bidiyon tsiraicin

Mai Shari’a Shu’aibu ya ce matasan sun adana tare da yada bidiyon tsiraici mai tsawon dakika 18 na wata matashiya a shafukan zumunta na Whatsapp da Instagram.

Sai dai bayan an karanta musu laifukan da aka fassara a harshen Hausa, matasan sun musanta aikatawa.

Daga nan ne lauyoyinsu, Barista Almustapha Abubakar  da Barista Shamsu Dauda suka bukaci a kawo shaidu ukun da ’yan sanda suka gabatar domin yi musu tambayoyi.

Kotun ta amince da hakan sannan ta dage zaman sauraron shari’ar zuwa ranar 3 ga watan Maris, 2021 domin sake sauraron bayanan shaidun.