Babbar Kotun Jihar Kano ta ci tarar Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje N800,000 bayan ya janye karar da ya shigar da jaridar Daily Nigerian da mawallafinta, Jaafar Jaafar kan zargin bata masa suna.
Ganduje dai ya kai Jaafar karar ne kan wasu bidiyo da jaridarsa ta wallafa inda aka ga Gwamnan yana zuba Daloli a aljihunsa, wadanda ake zargin na cin hanci ne.
- Cutar Shan-inna ta sake bulla a Jihohi 13 da Abuja
- Yaki da ta’addanci: Buhari na neman sojoji su canza salo
Da yake yanke hukunci a kan bukatar Jaafar na a biya shi da jaridarsa Naira miliyan 400 saboda bata masa lokaci, alkalin kotun, Mai Shari’a Suleiman Danmalam ya umarci Ganduje ya biya tarar saboda janye karar ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.
Lauyoyin Jaafar da Daily Nigerian, Ubi Eteng da Muhammad Da’Azumi tun da farko dai sun bukaci kotun ta umarci a biya wadanda suke karewa Naira miliyan 400 saboda bukatar mai kara ta janye karar ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.
Sai dai lauyan Gwamna Ganduje, O.E.B Offiong (SAN) ya bukaci kotun da ta yi watsi da bukatar biyan tarar tun da dai sun shigar da wata karar ta daban, inda ya ce kamata ya yi a jira sai lokacin da waccan kotun zata yanke nata hukuncin.
Sai dai Jaafar ya bukaci kotun ta ayyana cewa karar ta Ganduje ba ta da tushe ballantana makama.
Daga nan sai ya bukaci kotun da ta tilasta wa Gwamnan neman afuwarsa a bainar jama’a cikin akalla jaridun kasa guda biyu saboda yunkurin bata masa suna ta hanyar shigar da karar da bata da tushe.
Ya kuma bukaci kotun da ta hana Gwamnan daukar kowanne irin mataki da kansa ko ta hanyar wasu na shigar da kowacce irin kara a kansa kan batun bidiyon Dalar a nan gaba.
Sai dai alkalin ya ce za a saka sabuwar rana domin sauraron sabuwar bukatar ta Jaafar lokacin da bangarorin biyu suka shirya.