Jam’iyyar APC reshen Jihar Kano ta yi bukaci tsohon Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje da ya yi watsi da sammacin da aka yi masa kan bidiyo Dala.
A ranar Alhamis ce Hukumar Karbar Korafe-Korafe da Yaki da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta yi sammacin Gwamnan kan bidiyon.
- Bidiyon Dala: Muhuyi ya yi sammacin Ganduje
- Binciken kwakwaf ya nuna bidiyon Dalar Ganduje gaskiya ne – Muhuyi
Shugaban hukumar, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ne ya yi sammacin tsohon Gwamnan.
A shekarar 2017 ne jaridar intanet ta Daily Nigerian, ta wallafa wasu jerin bidiyoyi da ke nuna tsohon Gwamna Ganduje yana cusa Dalar Amurka a aljihunsa.
A cewar jaridar, kudin cin hanci ne. Amma Ganduje ya musanta hakan.
Sai a ranar Larabar nan, Barista Rimin Gado ya sanar da cewa binciken kwararru ya tabbatar da ingancin bidiyon.
Da safiyar Alhamis kuma ya ce ya aike wa Ganduje sammaci domin ya amsa tambayoyi a gaban hukumar.
To sai dai a wata tattaunawarsu da gidan talabijin na Channels a ranar Alhamis, Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, da Mataimakinsa, Ibrahim Zakari Sarina, sun ce bita da kulli kawai ake so a yi wa tsohon Gwamnan.
A cewarsu, sun fahimci gwamnatin Jihar ta jam’iyyar NNPP ce ke ingiza batun, wanda yanzu haka yake gaban kotu, domin ta bata masa suna.
APC ta ce an yi amfani da irin wannan shirin wajen kawo wa takarar Ganduje ta Gwamnan Kano karo na biyu a 2019 tangarda, amma ba ta yi nasara ba.
Jagororin sun ce a wannan karon, burin masu iza wutar binciken na kokarin ganin sun shiga tsakanin Ganduje ne da Shugaban Kasa Bola Tinubu.