✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bidiyon Dala: Muhuyi ya yi sammacin Ganduje

Shugaban Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa ta jihar Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ya yi sammacin tsohon gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje…

Shugaban Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa ta jihar Kano, Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ya yi sammacin tsohon gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje domin bada bayani game da bidiyon Dala.

A shekarar 2017 ne jaridar intanet ta Daily Nigerian, ta wallafa wasu jerin bidiyoyi dake nuna Gwamna Ganduje ya na cusa Dalar Amurka a aljihunsa.

A cewar jaridar kuɗin cin hanci ne amma Gwamna Ganduje ya musanta.

Binciken kwakwaf ya nuna bidiyon Dalar Ganduje gaskiya ne – Muhuyi

Ban damu da binciken bidiyon Dala ba – Ganduje

Sai a ranar Larabar nan, Barista Rimin Gado ya sanar da cewa binciken ƙwararru ya tabbatar da ingancin bidiyon.

Da safiyar Alhamis ɗin nan kuma ya ce ya aikewa Gwamna Ganduje sammaci domin ya amsa tambayoyi gaban hukumar.