✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ban damu da binciken bidiyon Dala ba – Ganduje

Tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya ce bai damu da matakin da hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa ta jihar ta ɗauka…

Tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya ce bai damu da matakin da hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da rashawa ta jihar ta ɗauka na ci gaba da binciken bidiyon da ake zargin an nuna shi ya na karɓar cin hanci.

Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimin Gado wanda Ganduje ya dakatar da shi kuma gwamnan mai ci, Abba Kabir Yusuf ya mayar da shi bisa umarnin kotu ne yace zai ci gaba da binciken.

Sai dai kwamishinan labarai na zamanin mulkin Ganduje, Muhammad Garba yace ko kusa binciken bai tayar musu da hankali ba.

Bidiyon Dala: Muhuyi zai binciki Ganduje

Ganduje na son kotu ta hana EFCC bincikensa kan bidiyon Dala

”Magana ce ta kotu,kuma shi Muhuyi a matsayinsa na lauya ya fi kowa sanin me ya kamata ya yi, mun zuba ido mu ga abun da za su yi, idan yana da dama ya binciki maganar da ke kotu ya fi kowa sani, idan ma ba shi da dama ya fi kowa sani”.

Ya kara da cewa ”ko da na yi magana da gwamnan Ganduje abun bai dame shi ba, saboda haka wannan lamari ne na shari’a.

Tsohon kwamishinan ya ce idan an gayyaci tsohon gwamnan domin neman bahasi zai yi shawara da lauyoyi kan matakin da ya kamata ya ɗauka.

Kwanan nan dai Ganduje ya buƙaci kotu ta dakatar da EFCC daga binciken bidiyon dalar saboda a cewarsa hukumar ba ta da hurumin gudanar da binciken.