Babbar Kotun Jihar Kano ta dage shari’ar zargin tsohon gwamna, Abdullahi Ganduje da iyalansa da wasu makusantansa da cin rashawa da karkatar da kadarorin gwamnati.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Usman Malam Na’abba, ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 16 ga watan Mayu, 2024, bayan sauraron bangarorin da ke shari’ar kar bukatar mika wa wadanda ake zargi sammaci, ba gaba da gaba ba.
Bayan zaman na ranar Litinin, lauyan gwamnatin Kano da ke karar su Ganduje, Barista Usman Umar Fari, ya bayyana cewa a zama na gaba ne alkali zai bayyana matsayarsa bayan sauraron jawabin bangarorin.
Idan ba a manta ba, kotun ta gaza zamanta na farko ranar 17 ga wata ne saboda gazawar bangaren gwamnati wajen ba wa wadanda ake kara takardar sammaci.
- Kwamitin Binciken Ganduje Kan harkallar kadarorin gwamnati ya fara zama
- Kanawa 19 sun mutu a hatsarin motar Dangote a Kogi
Lauyan ya bayyana cewa, a kan haka ne alkali ya saurari hujjojin bangarorin biyu kan halasci ko haramcin mika sammaci ga wanda ake kara a shari’ar tuhuma, ba kai-tsaye ba.
A cewarsa, bangarensu sun bayyana wa alkali hujjojin da suke ganin ya halasta a bisa doka a mika wa wanda ake zargi a irin wannan shari’a sammaci ba kai tsate ba, amma bangaren wadanda ake kara sun soke hakan.
Gwamnatin Kano ta hannun hukumar yaki da rashawa ta jihar na zargin gwamantin Ganduje da karkatar da kudaden kananan hukumomi da wasu makudan kudade hadi da kadarorin gwamnati.