Ministan Tsaron Chadi, Daoud Ibrahim da Sakataren Gwamnatin Kasar, Haliki Choua Mahamat, sun ajiye ayyukansu bayan fitar wasu bidiyoyinsu na batsal guda biyu.
Rahotanni sun ce jami’an gwamnatin sun ajiye aikin nasu ne a ranar Laraba, bayan bidiyoyin nasu sun karade gari musamman a kafafen sada zumunta na zamani.
- Majalisa ta yi watsi da kudurin bude iyakar Najeriya da Nijar
- Amurka ta goyi bayan Isra’ila kan harin da ya kashe mutum 500 a asibitin Gaza
Kakakin Firaministan kasar, Saleh Kebzabo ne ya ce gwamnatin ta amince da ajiye aikin nasu, kodayake sanarwar ba ta yi cikakken bayani ba.
Bidiyoyin dai da aka yada a ranakun Lahadi da Litinin, sun nuna mukarraban gwamnatin suna mu’amala da wasu.
Sai dai kamfanin dillancin labarai na Reuters bai iya tabbatar da sahihancin bidiyoyin ko jin ta bakin tsofaffin jami’an gwamnatin domin su mayar da martani a kai ba.
Ba kasafai dai ake samun badakalar fitar bidiyoyin batsa ba a Chadi, wacce galibin ’yan kasar Musulmai ne.
(NAN)