Shugaban Amurka Joe Biden na shirin kai ziyara Poland a Juma’a mai zuwa domin ganawa da shugaba Andrzej Duda kan mamayar da Rasha ke yi a Ukraine.
Fadar White House da ke sanar da wannan mataki ta ce Biden zai fara ganawa da shugabannin kasashe kawayen Amurka gabanin ziyarar zuwa Poland da ke da nufin samar da ayyukan jinkai ga ’yan gudun hijirar Ukraine.
A cewar sanarwar mai dauke da sa hannun Kakakin Fadar White House Jen Psaki ta ce Biden zai gana shugabancin NATO da na G7 da kuma EU gabanin ziyarar a Poland, don tattauna yadda za su bullowa Rasha a abin da ya kira zaluncin da ta ke aikatawa a Ukraine.
Psaki ta ce za su ci gaba da jan hankalin Duniya don ganin sun ci gaba da samun goyon baya ga al’ummar Ukraine tare da sukar shugaba Vladimir Putin na Rasha.
Sai dai Psaki ta ce ziyarar ta Biden ba ta da shirin kai shi zuwa Ukraine don ganewa idonsa yakin, sabanin shugabannin Poland da Czech da kuma Slovakia da suka je har Kyiv don ganewa idonsa yadda yakin ke gudana.