✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Biden zai tallafa wa sojojin Ukraine da Dala miliyan 800

Hakan na nufin tallafin Amurka a Kasar ya kai Dala biliyan bakwai tun hawan Biden

Shugaban Amurka, Joe Biden, ya ce nan ba da jimawa ba zai sake bai wa sojojin Ukraine karin tallafin Dala miliyan 800 a ci gaba da yakin da suke gwabzawa da Rasha.

Idan hakan ta tabbata, a jimlance zai kama kusan Dala biliyan bakwai ke nan da Amurka ta ba Ukraine tun bayan da Joe Biden ya kama mulkin Amurka.

Biden ya ce, tallafin wanda za a sanar a cikin kwanaki masu zuwa, zai hada da na’urorin tsaron sararin samaniya na zamani da manyan makamai, yayin da Ukraine ke ci gaba da fuskantar hare-haren Rasha a yankin gabashin Donbas.

Shugaba Biden ya ce, “Amurka na ci gaba da hada kan duniya don goya wa Ukraine baya,” tare da cewa zai ci gaba da ba da tallafin a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Biden ya yi wadannan bayanan ne a wajen babban taron kungiyar kawancen tsaro ta NATO wanda ya gudana a birnin Madrid na kasar Spaniya inda kasashe 30 suka yi ittifaki kan samar da sabon tsarin da zai mayar da hankali kan barazanar da Rasha ke yi.

Haka nan, Shugaban na Amurka bai rasa ta cewa ba game da gazawar da wasu kasashe kawayen Amurka ne ganin ya yi kan magance matsalolin da suka shafi cikin gida, ciki har da tashe-tashen hankula da hauhawar farashin kayayyaki da sauransu, inda suke ganin Biden din ya gaza cika alkauran da ya dauka na sake tabbatar da shugabancin Washington a idon duniya.

Ya ce “Amurka ta samu daidaiton da za ta jagoranci duniya fiye da kowane lokaci.

“Babu wanda ya zo ya same ni, ko kuwa dai kun ji suna cewa wani abu koma bayan godiya ga salon shugabancin Amurka…,” inji shi.