✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Biden ya lashe zaben shugaban Amurka

Biden ya kayar tsohon ubangindansa Trump domin zama Shugaban Amurka na 46.

Joe Biden ya lashe zaben Shugaban Kasar Amurka da gagarumar nasara.

Sanata Biden ya kayar da shugaba mai ci, Donald Trump mai hankoron yin tazarce a zaben da aka gudanar ranar 2 ga watan Nuwamba.

Shugban Amurka na 46 mai jiran gado tsohon Mataimakin Shugaba Trump ne da suka raba gari suka kuma jima suna zaman doya da manja.

Ya lashe zaben ne bayan fintinkau da ya yi wa tsohon ubangidan nasa wanda da farko ya yi ikirarin nasara.

Shugaban ya kuma garzaza kotu yana neman a hana ci gaba da kirga kuri’un a yankunan da yake ganin Biden ya samu kuri’u fiye da yadda ya yi zato; amma kotun ta yi watsi da karar.

Mummunan kaye da ya yi ta yi wa Trump musamman a yankunan dan kowannensu ke bukata ya mayar da Mista Trump abin zolaya ga Amurkawa.