Biyu daga cikin masu neman Shugabancin Majalisar Wakilai ta 10, Aliyu Betara da Yusuf Gagdi, sun janye wa Abbas Tajuddeen kamar yadda uwar jam’iyyar APC ta bukata.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar tasu ne dai suka bukaci sauran ’yan takarar su janye wa Abbas din.
- Nigeria Air: Ko sisi ba mu kashe ba wajen dauko hayar jirgin Habasha – Sirika
- Saudiyya ta ware Naira biliyan 46.6 don kafa masana’antar shirya fim
Kazalika, jam’iyyar ta tsayar da Benjamin Kalu a matsayin wanda zai yi wa Abbas din Mataimaki.
A baya dai ’yan takarar sun tsaya kai da fata cewa ba za su janye ba, sai dai a shiga zabe.
To amma bayan wata tattaunawa da Shugaba Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima a ranar Lahadi, Betara da Gagdi sun ce sun janyewar wa Abbas takarar tasu.
Sun kuma bukaci zababbun ’yan majalisar daga jam’iyyar da su goyi baya tare da zabar ’yan takarar kamar yadda uwar jam’iyyar ta bukata.
Idan za a iya tunawa, a baya dai ‘yan takara uku, Alhassan Ado Doguwa da Abubakar Maki Elleman da Abdulraheem Olawuyi, sun janye wa Abbas din.
A ranar Talata ce dai za a rantsar da sabuwar majalisar ta 10 bayan karewar majalisa ta tara, inda a nan ne kuma za a zabi sabbin shugabannin.