Dan wasan gaba na Faransa da ke murza leda a Real Madrid, Karim Benzema, zai gurfana gaban kotu a Larabar makon nan don fara fuskantar shari’a kan zarginsa da bata sunan tsohon abokin wasansa a tawagar kasa, Mathieu Valbuena.
Masu shigar da kara na tuhumar Benzema da yi wa Valbuena barazana ta hanyar amfani da wani hoton bidiyon batsa da ya nada shekaru 6 da suka gabata lokacin da suke taka leda a tawagar kasa.
- Harin Sakkwato: Lokacin kawo karshen ’yan bindiga ya yi — Buhari
- Za a binciki dan sandan da ya ‘kada kuri’a’ a zaben APC na Kano
Benzema mai shekaru 33, ana zarginsa da taimaka wa wani ayarin masu bata suna samun hoton bidiyon da nufin karbar makudan kudi daga hannu Valbuena.
Wannan takaddama a wancan lokaci ita ta zama dalilin da ya sanya ’yan wasan biyu wato Benzema da Valbuena mai shekaru 37 rasa gurabensu a tawagar kwallon kafar kasar gabanin dawo da Benzema a bana.
Bayanai sun ce tun farko wani matashi da aka bayyana sunansa da Axel Angot da wani Mustapha Zouaoui ne suka bukaci Valbuena ya biyasu wasu kudi ko kuma su saki bidiyon a Intanet.
Kamar dai yadda sashen Hausa na Rediyo Faransa ya nado wannan rahoto, ya ce wannan bidiyo wasu bayanai sun ce matasan biyu sun sameshi ne da taimakon Benzema.