Benzema ya ci gaba da nuna cewa shi gwarzon dan wasan Real Madrid ne, inda a yanzu ya zarce yawan kwallaye 350 da ya jefa wa kungiyar bayan samun nasarar taimaka mata wajen lallasa Almeria.
Kyaftin din wanda ya karbi rigar tunawa da kafa tarihin wannan bajinta daga shugaban kungiyar Florentino Pérez, ya zura kwallaye uku rigis yayin fafatawar ranar Asabar wadda Madrid ta doke Almeria da ci 4-2 a Bernabeu.
- Zan ci gaba da biyan albashin ’yan sandan da aka kora daga aiki —Rarara
- An yi wa kananan yara 2 yankan rago a Filato
A yanzu Benzema ya ci wa Madrid kwallaye 352 a cikin wasanni 642 da ya haska a kakar wasanni 14 da ya yi a kungiyar.
Babu shakka a yanzu shi ne dan wasa na biyu a mafi zira kwallaye a tarihin Madrid inda ya biyo bayan Cristiano Ronaldo mai kwallaye 451, wanda wadansu masu lura da sha’anin tamaula suke yi wa lakabi hantsi leka gidan kowa, kasancewar babu kungiyar da Ronaldon bai jefa wa kwallo ba a zamanin da yake Madrid.
Bisa yadda alkaluma suka nuna, kawo yanzu kwallayen da Benzema ya ci wa Madrid sun hadar da 236 a La Liga, 78 a Gasar Zakarun Turai, 25 a Copa del Rey, 25 a gasar Spanish Super Cup, 4 a Club World Cup da 2 a European Super Cup.
Benzema ya zama dan wasa na hudu mafi yawan zura kwallaye a tarihin La Liga
Yanzu dai Benzema shi ne dan wasa na hudu da ya fi zura kwallo a raga a tarihin gasar Sifaniya ta La Liga da kwallaye 236.
Karim Benzema wanda dan wasan Faransa ne mai rike da kambun Ballon d’Or na shekarar 2022, ya wuce dan Mexico, Hugo Sánchez mai 234.
Kyaftin din yana bayan ’yan wasa uku ne kawai: Zarra (251), Cristiano Ronaldo (312) da Messi (474).
Bayan nasarar da Madrid ta yi a kan Almeria, Benzema ya zama dan wasan kungiyar na biyu mafi samun nasarar wasanni a tarihinta.