✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Benzema ya buga wa Madrid wasa 500

Karim Benzema dan asalin Faransa kuma dan kwallon gaba a kulob din Real Madrid na Spain ya shiga kundin tarihi a kulob din bayan ya…

Karim Benzema dan asalin Faransa kuma dan kwallon gaba a kulob din Real Madrid na Spain ya shiga kundin tarihi a kulob din bayan ya kasance na 14 a jerin ’yan kwallon kulob din da suka buga wa kulob din wasa sau 500 ko fiye da haka.  Benzema ya samu wannan nasara ce bayan ya buga wasan El-Clasico a tsakanin Real Madrid da FC Barcelona a ranar Lahadin da ta wuce.

Sauran ’yan kwallon da suka shiga kundin tarihi a kulob din sun hada da Raul wanda ya yi wasa  741 da Casillas mai 725 da Sanchis mai 710 da Santillana, 645 da Ramos, 638 da Hierro, 601 da Gento, 600 da Camacho, 577 da Pirri, 561 da Michel, 559 da Guti, 542 da Roberto Carlos, 527 da kuma Marcelo, 503.

Rahotanni sun ce Benzema ya zura kwallo 240 sannan ya lashe kofuna 18 kawo yanzu a kulob din Madrid.