A yayin da kasashen duniya suka gudanar da wasanni daban-daban da suka hada da na sada zumunta da kuma na hayewa gasar cin kofin duniya da na Afirka a karshen makon jiya, ’yan kwallo da dama ne suka samu raunuka a yayin wasan al’amarin da ya sa kococi da dama suka shiga halin damuwa ganin yau Juma’a ne za a cigaba da gasar rukuni-rukuni a sassan duniya.
Kafar watsa labaran wasanni ta Goal.com ta tattaro sunayen ’yan kwallon da ba za su yi wasa a wannan mako ba kamar haka:
Holland: Masu tsaron gida (Goalkeepers) ’yan asalin Holand Jasper Gilessen da ke yi wa kulo din Ajad na Holland kwallo da kuma Tim Krul golan kulobh din Newcastle United da ke Ingila sun ji ciwo ne a lokacin da Holand ta yi wasa da Kazakstan. Don haka da wuya gololin su yi wa kulob dinsu wasa a wannan mako saboda raunin da suka samu. A Brazil kuma, dan kwallon bayansu Dabid Luis da ke yi wa kulob din Paris Saint Germain (PSG) na Faransa kwallo ya ji rauni al’amarin da ya sa aka canza shi a wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da kasarsa ta yi da ta Chile. Shi ma ana ganin ba zai bugawa kulob din PSG wasa a gasar rukuni-rukuni na Faransa a wannan mako ba.
Daga Sifen kuma an samu labarin jin ciwon Albaro Morata ne a lokacin da dan kwallon yake yi wa kasar haihuwarsa Sifen wasa a karshen makon jiya sai dai wani rahoto ya ce ciwon da dan kwallon ya ji bai yi tsanani ba, don haka akwai yiwuwar ya yi wasan gobe a tsakanin kulob dinsa na Jubentus da kuma na Inter Milan a gasar rukuni-rukuni na Italiya. Haka shi ma dan kwallon Sifen Dabid Silba ya ji ciwo kuma alamu sun nuna da wuya ya buga wasan Manchester United da na Manchester City a gasar rukuni-rukuni na Ingila. dan kwallon ya samu rauni ne a wasan Sifen da Ludemburg a karshen makon jiya.
A Jamus kuma, an samu rahoton dan kwallon tsakiyarsu da yanzu haka yake kwallo a Manchester United Bastien Schweinsteiger ya ji ciwo a lokacin da suke atisaye kafin wasan Jamus da Republic of Ireland. A wasan Republic of Ireland ce ta samu nasara a kan Jamus da ci 1-0. Shi ma dan kwallon Bayern Munich na Jamus Mario Gotze ya ji ciwo a wasan na Republic of Ireland. Rahoton ya nuna Gotze zai shafe makwanni 12 yana jinya.
A Faransa kuma, an ruwaito Karim Benzema wanda ya jefa kwallaye biyu a ragar Armeniya an canza shi daga bisani bayan ya samu rauni a wasan. Rahotanni sun nuna dan kwallon zai shafe makwanni uku yana jinya. Haka shi ma dan kwallon Faransa Paul Pogba da yake yi wa kulob din Jubentus na Faransa kwallo an ruwaito ya ji rauni a lokacin da yake atisaye kafin a fara wasan Faransa da Armeniya a karshen makon jiya.
Sannan dan kwallon Ajantina Sergio Aguerro ya ji rauni a daidai minti na 20 a lokacin da kasarsa ke wasa da ta Ekwado. An ce dan kwallon zai shafe kimanin makwanni 4 yana jinya. Kenan kulob din Manchester City na Ingila zai yi rashinsa musamman ganin yana da wasanni masu zafi a gasar rukunin firimiya na Ingila da kuma na gasar zakarun kulob-kulob a Nahiyar Turai (UEFA Champions League).
Benzema da Aguerro na cikin ’yan kwallon da suka ji rauni a makon jiya
A yayin da kasashen duniya suka gudanar da wasanni daban-daban da suka hada da na sada zumunta da kuma na hayewa gasar cin kofin duniya…