Real Madrid ta ajiye dan wasan gabanta, Karim Benzema, daga jerin ’yan wasan da za su kara a wasanta da Athletic Bilbao a zagayen ‘Quarter-Final’ na gasar Copa del Rel a daren ranar Alhamis.
Madrid ta ajiye dan wasan ne a sakamakon rauni da ya samu a wasanta na karshe da Elche, wanda hakan ya sa kungiyar ba za ta yi kasadar sanya shi a wasan ba tare da ya murmure yadda ake so ba.
- Bayan fuskantar jan kafa daga China, Buhari zai koma kasashen Turai da ciyo bashi
- Kisan Hanifa: An mayar da shari’ar gaban Babbar Kotu
Yayin tattaunawarsa da manema labarai, kocin kungiyar, Carlo Ancelotti, ya ce yana sa ran Benzema zai murmure kafin zuwa filin wasa na San Mames.
Sai dai Ancelotti ya ce Madrid ba za ta yi kasadar sanya shi ya buga wasa ba matukar bai murmure yadda ya kamata ba.
Benzema na kan ganiyarsa a bana, inda ya jefa kwallo 24 a wasanni 28 da ya buga daga kowace a gasa.
Kazalika, Madrid ba ta sanya sunan Benzema a cikin jerin ’yan wasan da za su kara da Bilbao ba, wanda ta saki a ranar Laraba.
Dan wasan na burin murmurewa baki daya kafin karawar Real Madrid da PSG a Gasar Kofin Zakarun Turai, nan da mako biyu masu zuwa.
Mariano Diaz da Ferland Mendy, kowannensu na fama da rauni, yayin da Marcelo ba zai buga wasan ba sakamakon dakatar da shi da aka yi na wasa uku.