✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Benuwe: Har yanzu ba a gano wasu mutanen ƙauyuka ba – Gwamna Alia

A halin da ake ciki, Gwamnan Jihar Benuwe, Hyacinth Alia ya bayyana cewa har yanzu ba a gano wasu mutanen ƙauyen ba bayan harin.

Rundunar ’yan sandan Jihar Benuwe a ranar Alhamis ta tabbatar da cewa an samu kwanciyar hankali a unguwar Otobi da ke Ƙaramar hukumar Otukpo biyo bayan wani mummunan hari da ya tilastawa mazauna garin barin gidajensu.

Kakakin rundunar ’yan sandan, CSP Catherine Anene a wata tattaunawa ta wayar tarho da wakiliyarmu, ta kuma yi watsi da rahoton sabbin hare-haren da aka kai kan unguwannin Emichi, Okpomaju da Odudaje, inda ta bayyana su a matsayin rahoton ƙarya don yawo tsoratar da jama’a.

“Unguwar Otobi yanzu akwai kwanciyar hankali, mun bar wasu jami’anmu tun ranar Laraba ana gudanar da bincike,” in ji Anene.

A halin da ake ciki, Gwamnan Jihar Benuwe, Hyacinth Alia ya bayyana cewa har yanzu ba a gano wasu mutanen ƙauyen ba bayan harin.

“Mun yi asarar mutane 11. Mun tura ƙarin jami’an tsaro,” in ji gwamnan yayin wani taron manema labarai inda ya bayyana hare-haren a matsayin batun ƙwace fili.”

Da yake mayar da martani kan wannan ci gaban, Sanata mai wakiltar mazaɓar Benuwe ta Kudu kuma shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa, Abba Moro ya yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta ci gaba da gazawa wajen kare rayuka, al’ummarsa za su iya amfani da hanyoyin kare kansu.

Sanatan, a cikin wata sanarwa da Emmanuel Eche’Ofun John, mashawarcinsa kan harkokin yaɗa labarai ya fitar, ya bayyana cewa hare-haren da suka janyo asarar rayuka da dukiyoyi na biliyoyin Naira abu ne da ba za a amince da su ba.

Ya kuma yi kira ga gwamnatoci a kowane mataki da su tashi tsaye wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya kuma yabawa Gwamna Alia da a ƙarshe ya fito ya yi Allah-wadai da wannan aika-aika a jihar, ya kuma buƙace shi da ya ƙara yi wa al’umma aiki, yana mai jaddada cewa ƙoƙarin gwamnati a dukkan matakai bai isa ba.

Moro ya kuma yi kira da a kafa sansanonin hukumomin tsaro a cikin unguwannin jama’a masu rauni