Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayar da sanarwar dakatar da shagulgulan bikin Kirsimeti da na sabuwar Shekara a dukkan kananan hukumomin Jihar 23.
Ya ce sun yanke shawarar ne a taronsu na Majalisar Tsaron Jihar da ya gudana a fadar gwamnatin jhar dake Makurdi.
- Boko Haram ta saki bidiyon daliban Kankara da ta yi garkuwa da su
- Shugaban Faransa ya kamu da COVID-19
- Duk da bude wasu iyakoki, har yanzu babu damar shigo da shinkafa da kaji
A cewar sa, saboda tabarbarewar al’amuran tsaro a fadin jihar, Majalisar ta yanke shawarar dakatar da bukukuwan a fadin jihar.
Ortom, ya shawarci mutanen jihar da su gudanar da bukukuwan nasu a gidajensu tare da bin shawarwarin da hukumomin kula da lafiya suka bayar na dakile yaduwar COVID-19.
Gwamnan ya kuma shawar ce su da su bayar da rahoton duk wani motsi da basu gamsu da shi ba ga hukumar tsaro mafi kusa da su.