✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bene mai hawa uku ya danne mutane da dama a kasuwar wayoyi ta Kano

Tun kafin yanzu an ankarar da masu aikin ginin kan tsagewarsa amma suka ce babu abin da zai faru.

Wani bene mai hawa uku da ya rufta a wata babbar kasuwar wayoyin salula da ke Jihar Kano ya danne mutane da dama.

Bayanai sun ce ginin ya rufta ne a kasuwar wayoyin salula ta Beirut Road, daya daga cikin manyan kasuwanni da ake hada-hada a birnin Dabo.

Wani ganau da ya zanta da wakilinmu, ya ce ginin wanda ya rufta fiye da sa’a guda da ta gabata, har yanzu ba iya ceto wadanda suka makale a karkashin baraguzansa ba.

Ya alakanta jinkirin da aka samu wajen ceto mutanen da rashin kayan aiki da za a iya yakice baraguzan ginin masu nauyin gaske.

A cewarsa, an jiyo muryar daya daga cikin wadanda tsautsayin ya auku a kansu kuma har yana iya amsa wayarsa ta salula yayin da aka kira.

“Yanzun nan muka kira layinsa kuma ya dauka. Sai dai ba shi da damar ceton kansa,” a cewar wani da lamarin ya faru a kan idonsa.

Sai dai wani daga cikin wadanda nauyin ceto ya rataya a wuyansu, ya ce manyan motocin hakar kasa na kan hanyar zuwa kasuwar a yayin da ake ci gaba da kai komo na ganin an ceto wadanda suka makale.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, ya zuwa yanzu an ceto wasu mutum uku da tuni an yi gaggawar mika su asibiti.

Wani daga cikin wadanda suke ba da gudunmawar aikin ceton ya ce, mutane da dama ciki har da mata da kananan yara suna makale a karkashin baraguzan gini, inda wasunsu ke kururuwar neman dauki.

Ya ce duk da tarin mutane sun hallara a wurin tare da nuna alhini, babu abin da za su iya aiwatarwa saboda babu wani dan Adam da zai iya dauke manyan baraguzan da suka danne mutanen.

Kazalika, ya ce babbar motar da aka kawo domin aikin yakice manyan baraguzan ita kanta lamarin ya fi karfinta.

“Wasu ’yan mata masu sayar da dafaffen kawai da mata masu sayar da abinci sun makale a karkashin ginin.

“Sai da muka haka rami sannan muka iya ceto mutanen uku su ma da kyar. Sauran suna karkashin ginin amma mun kasa gano hakikanin wurin da suke sai dai kawai muryoyinsu muke ji.”

A cewarsa, tun ba yanzu ba suka gano ginin benen ya fara tsagewa, lamarin da ya sanya suka ankarar da masu aikin kwangilar amma suka ce da su babu abin da zai faru.

Aminiya ta ruwaito cewa, daga cikin masu aikin ceton da suka hallara a wurin har da jamian Hukumar Kwana-Kwana, Hukumar Kiyaye Hadurra da ’Yan sanda da kuma jami’an Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa (SEMA).

Da yake zantawa da wakilinmu, Sakataren SEMA, Dokta Salahe Jili, ya ce suna ci gaba da yin duk wata mai yiwuwa domin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su.