✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bello Turji ya sake tsallake rijiya da baya a harin sojojin sama

Harin na zuwa ne bayan ya tsallake rijiya da baya a ranar Asabar

Jirgin sojojin saman Najeriya ya sake kai mummunan hari da safiyar Litinin kan maboyar rikakken dan bindigar nan, Bello Turji, a jihar Zamfara.

Aminiya ta rawaito yadda Bello Turjin ya tsallake rijiya da baya yayin wani harin da sojojin suka kai masa a gidansa ranar Asabar.

Wata majiya daga yankin ta shaida wa Aminiya cewa jirgin yakin ya sake dawowa da safiyar ta Litinin, inda ya jefa bama-bamai akalla guda biyu, da wajen misalin karfe 9:00 na safe.

A wani labarin kuma, wasu ’yan bindiga da ake zargin yaran Turjin ne sun kaddamar da hari kan matafiya a kan hanyar Sakkwato zuwa Gusau, a daidai garin Shinkafi na jihar Zamfara da safiyar Litinin.

Wani mazaunin yankin na Shinkafi, Murtala Wadatau, ya ce maharan sun tare hanyar ne a daidai garuruwan Kwanar Badarawa da Birnin Yero.