✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bello Turji ya rungumi zaman lafiya – Gwamnatin Zamfara

Gwamnatin ta ce hakan ya biyo bayan kwamitin zaman lafiyar da ta kafa

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce kasurgumin dan bindigar nan da ya addabi yankunanta da ma na makwabta, Bello Turji, ya karbi tayin zaman lafiyar da ta yi masa.

Mataimakin Gwamnan jihar, Sanata Hassan Nasiha ne ya bayyana hakan a Gusau, babban birnin jihar ranar Lahadi.

Ya ce tuban na Bello Turji ya sa yanzu an sami zaman lafiya a kananan hukumomin Birnin Magaji da Shinkafi da kuma Zurmi.

Mataimakin Gwamnan na jawabi ne yayin bude taron zaman lafiya da Kungiyar Daliban Jami’ar Madina da ke kasar Saudiyya ta shirya.

Hassan Nasiha ya ce shi da kansa ya tattauna da ’yan bindiga a kananan hukumomin jihar 14.

A cewarsa, “A wata ukun da suka gabata, an sami tsagaitawar kai hare-hare a gundumar Magami sakamakon yarjejeniyar zaman lafiyan da aka yi da ’yan bindiga.

“Kowa ya san kasurgumin dan bindigar nan Bello Turji da yadda yake cin karensa ba babbaka a yankin.

“Gwamnatin jihar Zamfara, ta hannun kwamitin zaman lafiyar da ta kafa, ta cim ma yarjejeniyar zaman lafiya da jagoran ’yan bindigar, kuma ya amince ya daina kai wa mutane hare-hare.

“Yanzu haka Turji ya koma kashe ’yan bindigar da suka ki tuba, suna kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba a kananan hukumomin Shinkafi da Zurmi da Birnin Magaji,” inji Nasiha.

Mataimakin Gwamnan ya kuma ce kwamitin ya tattauna da kungiyoyin ’yan bindiga har guda tara da ke masarautun Dansadau da Magami, inda suka bayyana korafe-korafensu.

Ya kuma shaida wa mahalarta taron cewa tuni gwamnatin jihar ta ba da umarnin dawo da burtalan kiwo, filaye da ruwa da sauran kayayyakin da aka kwace daga hannun makiyayan, inda ya ce dole bangarorin biyu su girmama yarjejeniyar muddin ana son ta dore.

(NAN)