Shugaban Ukraine Voladymyr Zelensky, ya ce shugaban Belarus Alexander Lukashenko, ya tura dakarunsa cikin Ukraine don taimaka wa na Rasha, wajen mamaye Ukraine.
Ita ma shugabar Malalisar Tarayyar Turai Verkhovna Rada ta tabbatar da labarin, inda ta ce Belarusawan sun kutsa kai Ukraine da safiyar Talatar nan.
Da farko dai Mista Lukashenko ya ce ba zai tura dakarunsa cikin kasar don mamaya ba kamar yadda BBC ya ruwaito.
Rahotanni dai na cewa dakarun Rasha na ci gaba da kusantar babban birnin Kyiv sannu a hankali.
Akwai babban aminci tsakanin shugaban na Belarus wanda shima yake fuskantar matsi daga asashen Turai da kuma shugaban Rasha Vladmir Putin.
A bayan nan ne Shugaba Zelinsky ya ce ya amince zai yi zaman sulhu da Rasha a wani wuri kan iyakar Ukraine da Belarus.
Mista Zelensky ya ce a tattaunawar da ya yi da shugaban Belarus Alexander Lukashenko, Ukraine ta amince ta gana da Rasha ba tare da wani sharadi ba a kan iyakar Ukraine da Belarus a kusa da kogin Pripyat.
Shugaban Ukraine ya ce Mista Lukashenko ya ce ya dauki alhakin tabbatar da dakatar da shawagin dukkanin jiragen sama, masu saukar angulu da masu kakkabo makamai mai linzami lokacin ziyarar domin tattaunawar tsakanin bangarorin biyu.
Sai dai gabanin amincewa da zaman, kasar Ukraine ta yi watsi da tayin da Rasha ta yi mata na hawa teburin sulhu da ita a kasar Belarus, inda shugaba Zelensky ya ce ya fi bukatar a tattauna a wata kasar sabanin Belarus.
Bayanai sun ce Belarus babbar aminiyar Rasha ce a yakin da take da Ukraine, wacce ake yi wa kallon ’yar kanzagin Rashar.
A ranar Lahadi ce Rasha ta sanar cewa ta tura wakilai Belarus domin tattaunawa da jami’an Ukraine.
Matakin watsi da tayin na zuwa ne yayin da Rashar ta shiga yini na hudu da kaddamar da hare-hare a kan kasar ta Ukraine.
Rahotanni sun ce kalaman na Shugaba Volodymyr na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Rasha ta ce tawagarta a shirye take ta hadu da ta gwamnatin Ukraine domin tattaunawa a birnin Gomel na kasar Belarus.
Rasha dai ta girke dubban dakaru a kasar ta Belarus tun ma kafin ta kai ga mamaye kasar ta Ukraine, inda Ukraine din ta zargeta da yin amfani da Belarus din a matsayin sansanin kaddamar mata da hare-hare.
A yanzu da aka kai shiga kwana na shida ana gwabzawa, tuni dai rahotanni suka tabbatar da cewa dakarun na Rasha sun shiga Kharkiv, birni na biyu mafi girma a Ukraine, a kokarinsu na danganawa da Kyiv, babban birnin kasar.