✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…BBC zai watsa gasar cin kofin nahiyar Afirka ga duniya

Kafar sadarwar BBC zai kawo cikakkun labarai kan gasar kwallon kafa na cin kofin Nahiyar Afirka karo na 30, wanda za a fara a gobe…

Kafar sadarwar BBC zai kawo cikakkun labarai kan gasar kwallon kafa na cin kofin Nahiyar Afirka karo na 30, wanda za a fara a gobe a Ekuatorial Guinea. BCC ya ce zai kawo rahotanni na musamman ne a kan kan ‘yan-wasa da kungiyoyin kwallon kafa ta rediyo, talabijin da kuma salula.

kwararrun masu sharhi kan kwallon-kafa na BBC za su rika kawo rahotonni kai tsaye daga garuruwa hudu da za su karbi bakuncin wasannin a kasar, da suka hada da Bata da Ebebiyin da Malabo da kuma Mongomo, sannan kwararrun za su rika bibiyar halin da kasashe 16 da za su fafata a gasar, tun daga zagayen farko a watan Junairu zuwa wasan karshe a ranar 8 ga watan Fabarairu.
Babu wani abu da kwararrun na BBC za su bari ba tare da sun taba a yayin gasar ba. Masu kallo da sauraro za su rika samun bayanai ne da dumi-duminsu tare da sharhi a kan duk wani wasa da za a yi.
Kafar sadarwar BBC ya ce zai kawo wasan bude gasar kai tsaye cikin harsunan Ingilishi da na Faransanci, a wasan da mai masaukin baki Ekuitorial Guinea za ta fara da Congo a babban filin wasan kasar ta Ekuitorial Guinea a ranar Asabar 17 ga watan Junairu. Sashin BBC mai watsa shirye-shirye a kasashen duniya, zai kawo wa masu saurare na nahiyar Afirka sharhi kai tsaye ta kafafen BBC Afrikue da BBC Swahili, dangane da manyan wasanni, tun daga wasannin dab-da-na-kusa-da karshe (kwata fainal) da na kusa da karshe (semi-fainal) da kuma wasan karshe (final)..
Masu amfani da wayar salula kuma za su samu bayanai ne kai tsaye daga kwararru kan manyan wasanni ta hanyar sharhi a rubuce.
Masu labaran wasanni na BBC za su rika kawo sharhi kan wasannin ta kafar tashoshin kawance na BBC da ke Afirka.
Masu san sauraron wasannin ko dai a Afirka ko a fadin duniya kuma za su iya samun bayanai da ma sharhi kan yadda wasannin suke tafiya daga tashar
rediyo ta Focus on Africa, a kowane lokaci daga cikin lokuta ukun da ake watsa shirye-shiryen,ko dai da karfe 1500 (uku agogon Najeriya) ko 1700 (biyar agogon Najeriya) ko kuma 1900 (bakwai agogon Najeriya) da agogon GMT.
Gasar za ta gudana ne a tsakanin ranakun 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabrairun 2015.