Ciwon tsoro na daya daga cikin cututtukan kwakwalwa da aka fi samu, wanda yawancin mutane ba su sani ba kuma yawancin masu matsalar ma ba su santa ba. Kai wasu masana ma sun ce a wasu al’umomin kamar a Turawa, wannan matsala ta sha gaban kowace matsalar kwakwalwa. Mu a irin al’umarmu, mata ne aka fi jin suna da wannan matsala ta ciwon tsoro, amma fa mazan ma kan samu.
Akwai tsoro akwai kuma Ciwon Tsoro. To a kimiyyance mene ne bambancinsu? Masana suka ce tsoro shi ne duk wani yanayi na razana yayin da mutum ya tsinci kansa a wani yanayi ko a gaban wani abu da bai saba gani ba, ko abin da aka fada masa cewa zai iya cutar da shi, ko ma dai wani abu da ransa ba ya so, ko da kuwa shi yana so.
Amma ciwon tsoro ya sha bamban da wannan yanayi ta fuskar cewa tsoron yana wuce misali, domin ban da razana, akwai fargaba da zulumi da damuwa da kan biyo bayan wannan yanayi, a wasu lokutan ma har da dimaucewa da shiga wani yanayi na rashin lafiya. Idan aka ji tsoron abin da bai ma kamata a ji tsoronsa ba, to shi ma zai iya shiga rukunin ciwon tsoro. Wadanda kuma suke samun wani babban tsoro da fargaba haka kawai ba tare da sun ga wani abu ba, su kuma ba ciwon tsoro ba ne da su, wani abu ne daban da ake ce wa ciwon fargaba (panic attack).
Misalin yadda ake gane bambancin tsoro da ciwon tsoro shi ne cewa idan gizo-gizo ya hau hannun mutum, to zai yi sauri ya fargita ya jefar da shi ko ya hure shi, shi ke nan ya wuce, watakila ma a yi raha da dariya, ba kamar yadda idan sha-zumamu (wanda yawanci ba a tsoronsa) ya hau hannu ba. To wannan tsoro ke nan. Ga mai ciwon tsoron gizo-gozo kuma, idan gizo-gizo ya hau hannunsa to bayan ya yi tsalle ya jefar da gizo-gizon, to za a ga alamun razana sosai a tare da shi, domin ko numfashinsa ma zai yi sama-sama, ya nuna alamun tashin hankali da damuwa, kamar karyowar zufa, kuka ko tashin tsigar jiki ko rawar jiki da sauransu.
Akwai ciwon tsoro iri-iri; Akwai ciwon tsoron shiga jama’a, wanda kusan shi ne kan gaba, akwai na tsoron magana a bainar jama’a, sai tsoron gizo-gizo, da ciwon tsoron hawa sama (kamar dogon bene ko jirgin sama), akwai na tsoron kaifi, wato duk wani abu mai kaifi, akwai na tsoron jini, wato rashin son ganin jini, akwai ciwon tsoron mage, wato kyanwa, akwai na tsoron tsuntsaye, akwai na tsoron kadaitaka, da na tsoron asibiti. Akwai su iri-iri.
Babban dalilin da ya sa aka kawo wannan maudu’i a yau shi ne cewa masu irin wadannan matsala da suke cikin al’umma amma ba kasafai suke son zuwa neman bayani ba, su san cewa an san da damuwarsu kuma akwai hanyoyin magance su idan suka nemi asibitin ma’aikatan lafiya na kwakwalwa. Yawanci ba magunguna ake bayarwa ba, dabaru ne na sauya tunani a kan abin da mutum ke samun tsoro da yawa a kai, amma idan abin ya kai wani matsayi watakila akan iya hadawa da magungunan.
Amsoshin Tambayoyi
Ni idan raina ya baci da na taba karfe sai na ji kamar wayar lantarki ta ja ni. Kuma idan na taba mutane sukan ce sun ji lantarki. Kuma idan na taba kusa sai ta karye, ni kuma ban sha tauri ba. Hakan lafiya ce ko rashinta? Mene ne abin yi?
Daga Bashar U. Daura
Amsa: E, kwarai a duniya akan samu mutane masu baiwa iri-iri, kamar irin wanda aka ba da labarinsa kwanan nan a kasar Masar, wanda aka ce yana da karfin doki 70 kuma yana iya balla kwandala da idanunsa. Kai ma watakila baiwa ce ke nan. A kimiyyance ma an san akwai mutane wadanda halittarsu ba daya take da ta sauran jama’a ba ta fuskar irin wadannan baiwa. Wannan ba za a kira shi ciwo ba sai dai baiwa, tunda za ka iya rayuwarka lafiya kalau ba tare da shan wasu magunguna ba.
Ni likita ina yawan samun jiri idan na kwanta ko na yi sujuda. Sai na ji kamar ina tafiya. Mece ce shawara?
Daga Umar S. Zariya
Amsa: E, akwai wasu kananan kasusuwa a cikin kunnuwanmu masu sa wa jikinmu daidaito yayin tashi, zama da kwanciya. Su wadannan kasusuwa su ke aikawa kwakwalwa cewa tafiya ake, ko zama ake ko kwanciya. To, amma yayin da suka dan samu tangardar sadar da wannan bayani sai kwakwalwa ta kasa gane ko a wane hali ake. An fi samun wannan a mutane masu yawan tafiye-tafiye da kuma masu ciwon kunne ko hawan jini. Don haka yana da kyau ka je asibiti a tantance mene ne, a yi maka gwaje-gwaje na kunnen da na hawan jini, da na jini a gano inda matsalar take. Idan aka gano ko mene ne, ko ma wace matsala ce, akwai maganin da za a iya ba ka ya daidaita matsalar.
Ni kuma jin jiri nake da gani dusu-dusu yayin mikewa. Ko mece ce matsalar?
Daga Khalid S. Keffi
Amsa: Kai ma kusan a iya cewa akwai alamun irin matsalar waccan tambaya ta sama, amma irin wannan raguwar zagayawar jini a kwakwalwa ce ta fi kawo shi. Don haka kai ma yana da kyau ka je a yi maka aune-aune irin na Malam Umar, a tantace matsalar.
Ni kuma bugun jinina ne kullum a kasa yake, za ka ga an auna an ce mini 100/70. Akwai shawara?
Daga Zuwaira, Zariya.
Amsa: E, akwai wadanda za a auna bugun jininsu a ga bai kai na sauran jama’a ba, kuma yawanci suna da kananan jiki, ko ba masu son cin abinci sosai ba ne, kuma ba su da wasu alamu na jin jiri ko yawan kasala. To idan haka ne babu damuwa, amma idan akwai alamu irin su jiri, ciwon kai, gani dusu-dusu, sai an dauki mataki an yi gwaje-gwaje an gano dalili.
A kwanakin baya an yi bayani a labarai cewa akwai magunguna fiye da kimanin dari hudu da ake hadawa da sayarwa a nahiyar Afirika. To likita me ya sa ba ku yi mana bayanin irin magunguna ne sai dai mu ji a labarai?
Daga Aminu Tudun Nufawa, Kaduna
Amsa: Ai idan da kana binmu yau da kullum, da za ka san alkiblar wannan shafi. A takaice dai alkiblar wannan shafi ba ta magunguna ba ce, alkbilar kiyayewa da magance matsalolin lafiya aka dauka, ta hanyar dabaru ba ta hanyar magani ba. Idan muka san abu dole sai an dangana ga magani, mukan ba da shawarar takamaimai wurin da ya dace ya nemi magani. A wasu lokuta can baya amma, mun hada kai da wasu masana magani (pharmacist) aka yi rubuce-rubuce a kan magungunan da za a iya samu a kayan abincinmu, domin irinku masu neman magunguna. Idan ka shiga shafin wannan jarida na yanar gizo ka laluba za ka gan su.
Nan gaba ma muna sa ran ba wasu masu ilmin magunguna dama su karemu. Don haka muna maraba da kuma barar rubutu daga duk wani masanin magani ko wata gudunmowa ta ilmin kiwon lafiya fayyatacce ba mai surkulle ba.