✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayanin likita dangane da ciwon Sanyin kashi

Hannuna ne guda daya ba na jin dadinsa kamar dayan kuma karamin yatsana ba ya motsi sosai. Shi ne nake ganin ko sanyi ne? Ko…

Hannuna ne guda daya ba na jin dadinsa kamar dayan kuma karamin yatsana ba ya motsi sosai. Shi ne nake ganin ko sanyi ne? Ko da wata shawara da za ka taimakan da ita?
Daga Shazali karambosuwa, Legas
Amsa: A makon da ya gabata mun yi magana a kan karayar kashi. Wani ciwo kuma da yake addabar kashi shi ne na sanyin kashi. To yana da kyau shi ma wannan ciwo a gane shi sosai. Ba kamar yadda wasu suke kiransa da ciwon sanyi ba, ciwon sanyi daban, na sanyin kashi daban. Ciwon sanyin shi ne wanda namiji ke sa wa mace ko kuma mace ta sa wa namiji. Sa’annan kuma don an ce sanyin kashi ba ana nufin yanayin sanyi ne ke sa ciwon ba, ciwon ne yake yi kamar sanyi.
To sanyin kashi yana da bambanci da karaya ko targade ko gocewar kashi. Shi sanyin kashi ba sandar kashin yake tabawa ba, karshen kashin wato gabobi yake kamawa. Abin da ke faruwa a gabobin shi ne, wasu sinadarai ko dai na jiki, ko na waje wadanda muka ci a abinci sukan taru a gabar su kumbura wurin, su sa ciwo, wani lokaci ma su ci kasusuwan wannan gaba.
Kowa zai iya yi, matasa, manya da tsofaffi, maza da mata, amma kananan yara ba su cika samunsa ba. Idan aka ga kumburi da ciwon gabobi a yara to a mafi yawa ciwon jini ne kamar sikila wato amosanin jini.
Alamomin kamar yadda ka fada ba dole sai an ji ciwo sosai ba, yawanci ji kawai za a yi wurin ba kamar yadda aka saba ba ko kuma idan bangare daya ya kama akan ji gabar ba kamar dayar ba, domin a wasu lokutan bangarori biyun ciwon yake kamawa. Sauran alamun su ne kumburi ko sandarewar gabar ta kasa motsi, ta yadda idan aka motsa sai an ji zafi. Abin da aka sani na dalilan wannan ciwo shi ne gado. Idan wani daga cikin iyaye ko kakanni ko ’yan uwa na jini suna da ciwon to kai ma ba makawa za ka iya samu.
Akwai sanyin kashi iri-iri. Kamar yadda muka zayyana a sama, yana iya kama kowa, amma an fi kasafta shi da wanda kan kama kowa da wanda kan kama tsoffi. Bari mu dauki wanda ya fi kama kowa wanda shi ake kira sanyin kashi na gout. Yakan zo idan wani sinadarin acid da jiki ke sarrafawa bayan mun ci abinci kamar nama da alayyahu (mai suna uric acid) ya taru a gabobi. To shi wannan sinadarin acid shi ne yake gwagwiye gabar kashin a hankali sai a ji duk alamun da ake ji. Ya fi kama kananan gabobi kamar gabobin yatsa na kafa.
Na tsoffi iri-iri ne amma an fi ganin iri biyu, su ma akwai na gado (rheumatoid arthritis), akwai wanda ba na gado ba (osteoarthritis). Na gadon ya fi kama kananan kashi na hannu, dayan kuma ya fi kama manyan gabobi.
Dukkansu dai sai an je asibiti an duba mutum an tantance tunda sukan yi kamanceceniya, kuma magungunansu daban-daban ne; duka dai akan iya ba mutum magungunan rage zogi da magunguna rage sinadaran a jini.
Da yake duk matsalolin gado ne, da wuya a warke gaba daya, sai dai ciwon ya lafa. Amma ana iya kiyaye tashin ciwon a gout misali. Idan mutum mai ciwon ko mai gadon ciwon ya rage cin jan nama da alayyahu (ya maishe su da farin nama da wani ganye daban) zai dade ciwon bai tashi ba.
Likita, na kai tsawon shekaru hudu ina fama da yawan ciwon kai. Mene ne yake kawo min ko kuma wani ciwo ne yake damu na?
Daga Bala Shamaki, Shendam
Amsa: A likitance ba za a iya cewa ga takamaimai abin da ke damunka ba kai tsaye da wannan dan bayani naka. Likitan zamani ba boka ba ne da zai ji bayaninka ya ce kawai e, wannan kari ne da kai ko ciwon daji. Akwai abubuwa da dama da sai an zauna da kai an tambaye ka kafin a iya gane wannan irin ciwon kai. karin bayani guda daya mai gamsarwa da ka zayyana, shi ne cewa ciwon kan ya kai shekaru hudu. To shi ma wannan bayani guntu ne, domin ana so a ji ko kana nufin tun da ya fara shekaru hudu bai daina ba har yau ko kuma yana lafawa ya dawo? To koma dai me ke faruwa irin wannan ciwon kai tabbas ba irin wanda ake samu ya tafi cikin ’yan kwanaki ba ne, irin na su Maleriya da Tafot. Manyan abubuwa da kan kawo ciwon kai irin naka su ne ciwon barin kai daya (migraine) da ciwon kai na gajiya (tension headache ko cluster headache).
Wannan dai hasashe ne, don haka ka je ka gana da likita kiri-da-muzu don ya yi maka wasu tambayoyi.
Me ke kawo fitsarin jini? Mene ne maganinsa?
Daga Tajuddeen D. Gwazaye
Amsa: Yawanci cututtukan matattarar fitsari da ke mara da fitsarin jini suke fara nuna alamu. Wato dai ga mai fitsarin jini tabbas akwai matsala a mafitsara, tunda kuma matsalolin mafitsara masu kawo fitsarin jini suna da yawa, ba a iya cewa ga daya ba, sai an bincike ka.
Likita ko da gaske ne maganin sauro na shafawa yana da illa ga fata?
Jamil Mai Magani, Malumfashi.
Amsa: kwarai kuwa wasu kalilan a mutane fatarsu ba ta karbi sinadaran da ke cikin irin wadannan mai ba, wato dai za a iya samun matsala ta kaikayi ko saba ko tsagewar fata idan sun yi amfani da shi. Don haka yana da kyau idan ka sayar da duk wani maganin shafawa ka fada wa mai sayen ya gwada a dan wuri kadan tukun ya ji, idan ba matsala a iya shafe duk jiki da shi.
Wane lahani gas din da ke cikin lemon kwalba ko na gwangwani ke haifarwa ga dan Adam idan ya sha shi kai tsaye?
Daga Sulaiman Kurma Dutsin-ma.
Amsa: Ba su da wani lahani na ku-zo-mu-gani, domin da hukumomin lafiya ba su yarda a sa su a abin sha ba. Sukan iya sa taruwar sinadarin acid da yawa dai a ciki, ta yadda mai gyambon ciki zai iya shan wahala idan ya sha.

LAFIYAR MATA DA YARA

A yau wannan fili zai amsa
tambayoyin da aka samu

Ciwon ciki nake idan na samu juna biyu. Ba zai daina ba har sai na haihu. To yanzu na samu wani, ciwon ya tashi; na je asibiti aka ce ciwo ne a bayan mahaifata sai an yi min aiki idan zan haihu a cire dan da ciwon gaba-daya. Suka ba mu lokaci mu dawo 3 ga watan 6 za suyi min aiki. To amma kafin lokacin sai na haihu 26 ga watan 5. To mun koma asibiti aka ba mu sikanin. Sai aka ce ciwon ya zama 2cm. To ni na kasa gane mai suke nufi da ni, don na san yadda nake jin ciwon. Daga W. M. Kaduna
Amsa: To da yake ke kin yi bayani mai dan gamsarwa, ba zai dauki lokaci ba a gane cewa alamu ne na karin mahaifa da kike da shi. Tun da asibiti ba su da lokacin zama su miki bayani (watakil domin dalilai na yawan marasa lafiya), bari na fahimtar da ke abin da suke nufi. Da farko dai karin karami ne, tunda ya bar ki kin samu juna biyu (akwai karin da zai girma ya cika gaba daya mahaifar a kasa samun juna biyu, wani lokaci ma a dauka juna biyun ne).
Na biyu kuma shi ne idan kika samu juna biyu, to abin da ke mahaifar yana danne karin shi ya sa kike jin zafi, da kin haife kuma an daina danne shi sai ya daina zafi. Na uku kuma shi ne da so aka yi idan kin zo haihuwa a miki tiyata su cire dan, a kuma cire karin, kin ga an harbi tsuntsu biyu ke nan da tsakuwa daya. Na hudu kuma shi ne da kika haihu kika dawo da hoton scanning sai hoton ya nuna ai karin karami ne girman 2cm kawai, wanda wannan bai kai a bude mahaifa a cire ba, sai ya kai kamar santimita 15 kafin a ce e, lallai kina bukatar tiyata. Idan kika ci sa’a, tunda karin yana kankancewa, zai narke, in kuma girma yake kara yi, sai an cire.
Me ya sa mace ke ciwon mara ko ba ta al’ada? Akwai matsala ke nan?
Daga Maijidda M. Kano da A’isha Sa’id Legas
Amsa: kwarai kuwa duk wani ciwon mara a mace idan ba al’ada ba ce ko nakuda, matsala ce. Don haka ki shafa wa kanki lafiya ki nemi dalili da kuma mafita.
Me ke kawo haki ga mace mai ciki?
Daga Hafsatu A. Usudu
Amsa: dayan uku, ko dai matar ba ta da isasshen jini a jikinta. wato abin da ke cikinta ya janye, wanda shi ne ya fi kawo hakan ko kuma ciki ya girma ya tokare huhu a kirji, ta yadda za a iya samun numfashi sama-sama musamman ma idan ta kwanta ko kuma zuciya ba lafiya.