✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayanin da wani malami ke yi cewa Al-Mustapha zai horar da makasa kazafi ne – Maiguduma

Wani malami mai suna Malam Muhammad Auwal Abubakar da ake wa lakabi da Maiguduma, ya yi Allah wadai da wani faifai da ke yawo a…

Wani malami mai suna Malam Muhammad Auwal Abubakar da ake wa lakabi da Maiguduma, ya yi Allah wadai da wani faifai da ke yawo a kasuwa inda a cikinsa wani malami mai suna Malam Sanusi Khalil ya ce dogarin marigayi Shugaban kasa Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha na horar da matasa dubu daya, don auka wa masu hamayya da Shugaban Goodluck Jonathan kafin zaben 2015, inda ya bayyana hakan a matsayin kazafi da ya saba wa shari’an Musulunci da dokar kasa.
Malam Maiguduma wanda ya bayyana haka a yayin zantawa da Aminiya, ya ce danganta Manjo Al-Mustapha da al’amarin idan ma har akwai shirin yin hakan, wani makirci ne da bi-ta-da-kulli da wasu da ke adawa da fitowarsa daga gidan kurkuku, suka kitsa da kuma ke da nasaba da siyasa. Ya ce ba daidai ba ne malami ya tsunduma kansa a ciki, inda ya bukaci al’ummar Musulmi da Kiristoci musamman talakawa su dawo daga rakiyar amfani da addini ko malamai wajen biyan bukatar siyasa, ya ce siyasar kasar nan ba ta ginu a kan tsarin addini ba.
Malamin ya ce abin da ya kamata talakawa mabiya addinan biyu su maida hankalinsu a kai shi ne zaben adalan shugabanni, sannan su yi watsi da azzulumai koda ’yan uwansu ne.