Mutum hudu a cikin kowadanne ’yan Najeriya 11 ke fama da cutar suga, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya.
Wadansu masu cutar ba su san suna da ita ba, wasu kuma ba su fahimci yadda take ba.
- Najeriya A Yau: Yadda cutar suga ta hana ni zama soja —Matashi
- Hanyoyi 9 da rashin samun isasshen barci ke cutar da dan Adam
Shugaban Kwalejin Koyar da Aikin Likita a Jami’ar Yusuf Maitama Sule, Farfesa Muhammad Kabir ya yi wa Aminiya bayanin cutar.
– Ku san cutar suga
Kwararren likitan a fannin kula da lafiyar al’umma ya ce cutar suga na samuwa ne ida yawan sukarin da jikin dan Adam (glucose) ke bukata ya wuce yadda jiki ke bukata.
“Kowa yana da shi da yadda Ubangiji Ya yi yadda zai kasance daidai; To amma idan ya yi sama, ya wuce wani awo shi ne ake cewa mutum yana da ciwon sukari.”
Ya kara da cewa ba a lokaci guda ake yanke hukuncin cewa mutum yana da cutar ba.
“Sai ya dade a rayuwar mutum, idan ana ganin koyaushe awon wannan nau’in sukarin ya yi sama, shi ne ake cewa mutum yana da ciwon sukari wato Diabetes Melitus.”
“Ta awo asibiti ne ake samun wannan nau’in sukari, idan aka ce kar a ci abinci, ka zo asibiti da safe aka dauki jini aka ga ya wuce awo 7.8… gaskiya za a ci kana da ‘Diabetes’.”
– Rabe-raben cutar suga
Cutar suga ta kasu gida biyar, bisa la’akari da abin da haddasa ta:
- Type 1 Diabetes: Tsananin karancin sunadarin da ke sarrafa glucose a jikin mutum.
- Type 2 Diabetes: Karancin aikin sunadarin da ke sarrafa sukari a jiki yadda ya kamata, “Amma dai ba a ce gaba daya babu ba.” Wannan shi ne ya fi yawa a cikin al’umma.
- Type 3 Diabetes: “Wanda mata in sun yi ciki sukan samu, sai dai yana bacewa bayan sun haihu.”
- Type 4 Diabetes: “Wanda idan mutum ya zauna cikin yunwa, ba samun abinci, shi ma wannan yana janyowa mutum ya kamu da ciwon sukari.”
- Type 5 Diabetes: “Shi ne wanda ke samuwa a sakamakon wasu cututtuka kama cutar hanta ko idan hakkin ciki (pancreas) ta samu cuta.
“Daga Pancreas ake samun sunadarin da ke sarrafa sukari a jikin mutum. Shi ma idan ya samu wata cuta musamman cutar kansa, ko ta shan magunguna da ake kira steroids, idan aka dawwam ana shan su,” inji Farfesa Muhammad.
– Yadda ake kamuwa da ita
Likitan ya bayyana cewa ana iya daukar cutar sukari daga wani, kuma “Duk cutar da ake iya dauka daga wani akwai maganar gado, daga iyaye.
“Kamar yadda cutar sikila take, ai dole sai ka dauki wata kwaya daga uba da wata kwaya daga uwa sun hadu.”
Bayan haka ana iya daukar cutar, “Ta wasu abubuwa da aka sani idan ka dawwama a kansu za su jawo cutar.
“Ko kuma idan ka shiga wani yanayi,” ko idan aka samu taruwar wasu dalilai kamar gado da sauransu.
– Alamomin cutar suga
Manyan alamomin cutar hudu ne:
- Tsananin jin kishirwa
- Yin fitsari mai yawa a lokaci guda
- Yawan shan ruwa da yawa
- Ramar jiki
– Maganin cutar
“Idan aka bi wasu hanyoyin kamar motsa jiki, rage kiba da kuma shan magunguna yadda aka kayyade, wannan duk zai iya dawo da nau’in sukarin da jikinka ke bukata — wanda in ya yi yawa yake kawo cutar sukari — ya koma daidai,” inji likitan.
– Shin ana warkewa?
Amma ya ce, “Babu zancen warkewa a ce ya bata, sai dai ka ci gaba da yi wadannan abubuwa: Kada ka sha sukari, lemon kwalba da kayan zaki.
“Idan za ka ci abinci kuma ya kasance abincin ‘Protein’ da ‘Carbohydrate’ da kitse ne, amma ba da yawa ba.”