Ba kamar sauran irin wadancan matsaloli da muka yi bayani a baya ba, shi faduwar gaba ba ciwo ba ne, sai dai a mafi yawan lokuta alama ce ta cewa akwai ciwon, domin wasu masu aiko da sakonni sun fara alakanta ta da ciwon fargaba da aka yi bayani a makon da ya wuce. A’a, akwai bambanci.
Ita faduwar gaba a saukake ana nufin aikin da zuciya kan yi da karfi kuma da sauri wato dukan uku-uku din nan da akan ce, wanda mutum zai iya ji. Duk aikin da zuciya take yi bai kamata mu ji ba, ko mu ji alamu, amma yayin da aka samu faduwar gaba, yawanci akan ji bugun ya fito fili. Za kuma a iya bambance shi da ciwon bugun zuciya wanda ke nufin tsayawar aikin zuciyar na wasu dakikoki, sakamakon rashin zagayawar jini cikin tsokar ita kanta zuciyar.
Faduwar gaba za ta iya zama alama ce ta ciwon zuciya ko kuma alama ta wani ciwon na daban, kamar ciwon makoko ko karancin jini a jiki da sauransu. Kai zai iya zama ma alama ce ta ciwon fargaba da ciwon yawan tsorata (phobia da panic attack) da aka yi bayaninsu. Sa’annan masu yawan shaye-shayen kayan maye da gahwa da shayi idan abin ya yi musu yawa sukan iya samun matsalar a kai-a kai. Akwai wasu magunguna ma na asibiti da na gida wadanda shansu kan iya kawo matsalar.
Don haka mai samun yawan samun faduwar gaba a kai-a kai haka, kawai ke nan shi ma dai zama bai same shi ba, sai ya samu lokaci ya je an duba shi an tantance dalilin samun faduwar gaban.
AMSOSHIN TAMBAYOYI
DABAN-DABAN:
Idan na tashi daga barci ko da a lokacin sanyi ne, nakan ji zafi ya rufe ni. Ina so a yi mini bayanin me ke kawo haka?
Daga Abdullahi, Kabo da Ibrahim Sarki, Kaduna
Amsa: Abubuwan da ke kawo yawan jin zafi ko da lokacin sanyi ne a akasarin lokuta, shi ne duk wani abu da zai taba lafiyar malolon wuya, wanda muka ce shi ne ke sakin sinadaran da jikinmu ke sa a ji dimi ko a ji sanyi a mabambantan yanayi, a kuma duk lokacin da bukatar hakan ta taso. Ka je asibiti a yi maka binciken lafiyar jiki da makokon, ka kuma ji sauran karin bayani a wurin likita idan sakamakon ya fito.
Shin akwai wata illa ga wanda yake yawan shan maganin gargajiya mai daci?
Daga Garba Sabiyola, Gashuwa da Junaidu Maicaji, Dutsinma
Amsa: A kullum in za ka ji mun lissafo abubuwan da ke jawo matsalolin lafiya, zai yi wuya ka ji ba mu sa yawan shaye-shayen magunguna barkatai ba. Wato yawan shaye-shayen magunguna barkatai, na asibiti ne ko na gargajiya, ba tare da shawarar ma’aikatan lafiya ba, ba ya cikin dabi’a mai kyau a tsarin kiwon lafiya.
Ni kuma sai na yi shekara ban yi wata rashin lafiya ba, ko da zazzabi, kuma ba wani magani da nake sha. Shin hakan lafiya ce ko kuwa?
Daga D. dankano da Imran Adam
Amsa: E, wannan kwarai za a iya cewa lafiya ce Allah Ya ba ku, ba rashin lafiya ba, don haka sai a rika gode maSa.
Ni kuma idan na hau keke na yi tafiyar kamar minti 30 ko fiye sai na ji wandona ya jike da gumi, kamar na zauna kan ruwa, amma wasu ba sa samun haka. Ko lafiya ce?
Daga Shamsuddeen
Amsa: E, kowa da irin yadda yanayin halittarsa take, akwai masu gumi ta kafafen fata mabambanta; wasu kan yi duk jikin, wasu a fuska, wasu a tafin kafa ko na hannu, wasu a kirji kawai, wasu ta hammata, wasu a matse-matsin cinyoyi. To ina ganin gumin da kake daga matse-matsin cinyoyi ne yake jika maka wando yayin tukin keke. Ba matsala ba ce da za ka damu da ita. Sai dai kawai idan abin na damunka ka rika shafa abubuwan da kan rage yawan zufa kamar hoda ko man roll-on, ko ka sa wani wandon a ciki irin skin-tight dinnan wanda zai tsane zufar a ciki, amma idan ba ka samu mai kyau ba shi ma zai iya kara maka yawan gumin.
Ni idan na ci awara ko kwai sai cikina ya kulle, na kasa zaune na kasa tsaye. Me ke kawo haka, kuma mene ne abin yi?
Daga Muhammad Abdullahi, Bauchi da Abubakar Aliyu, Gusau da A’isha Mainasara, Funtuwa
Amsa: Ai irin wannan tambaya mun sha amsa irinta Malam Muhammad. kwarai, akwai yadda jikin kowa ke karbar abinci daban-daban. An fi samun wannan matsala ta food allergy da abinci masu sinadarin gina jiki na protein irin wadanda ka lissafa, da wasu kamar su wake, wasu madara, wasu ma kifi ne jikinsu ba ya iya karba. Abin yi shi ne ka gane duk abin da jikinka ba ya so ka guje shi.
Me ya sa mutum a wasu lokutan kawai zai ji bai damu da cin abinci ba, ta yadda ko da ya fara ma da ya ci kadan zai bari?
Daga Arc. Muttaka Ibrahim
Amsa: kwarai, rashin son cin abinci da barin cin abincin da zarar an fara alamu ne na matsalar wata rashin lafiya. A ka’idar aikin jiki, kamata ya yi duk bayan wasu sa’o’i kamar daga awa hudu zuwa shida bayan abincin karshe da mutum ya ci, mutum ya ji yunwa ko sha’awar abinci. Wanda bai ji daya daga cikinsu ba, ko kuma ya ci kadan wanda bai taka-kara-ya-karya ba, ko da ba shi da wasu sauran alamu, dole ya je a binciki lafiyarsa. Amma a tsofaffi da masu ciki ana iya samun matsalar ba tare da wani ciwo ba.
Abokina ne ke da cin ruwa, ya yi amfani da magunguna amma har yanzu ba sauki; shi ne muke neman shawara Daga Shehi Imrana, Dutse
Amsa: To ai in dai Dutsen Jigawa ce, kuna da manyan asibitoci sosai, don haka ba damuwa. Idan cin ruwa ya yi kamari, ya ki jin maganin shafawa irin wadanda ake samu a kyamis ko da ba a rubuta wa mutum ba, irinsu man whitfield ointment ko man clotrimazole da na miconazole, dole ne ya nemi inda zai ga likitan fata, wadanda na san akwai a manyan asibitocinku
Ni kuma fatata ce ta fuska ke yawan tattarewa, kamar ba ta da kwari. Mece ce matsalar kuma mene ne abin yi? Daga K. I Tarauni
Amsa: Kai ma yana da kyau ka dangana ga likitan fata, a babban asibiti mafi kusa da kai domin ya gani, tunda an ce gani ya kori ji. Yawanci wasu shafe-shafen ba gaira-ba-dalili da tsufa ne suka fi sa haka.