Bayan wata 11 ana fuskantar hauhawar farashin kayyaki a Najeriya, a karon farko ya fado da kashi 21.34 cikin 100 a watan Disamban 2022, in ji Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS)
Hukumar ta ce alkaluman sun fado ne daga kaso 21.47 da suka yi a watan Nuwamban bara.
- Kotu ta yanke wa mutum 6 hukuncin kisa ta hanyar rataya a Osun
- NAJERIYA A YAU: Wanne hali matan da mazansu sojoji suka mutu suke ciki?
NBS ta bayyana haka ne ranar Litinin, cikin rahoton karshen wata da ta saba fitarwa, inda ta kara da cewa farashin kayan abinci ma ya sakko da kashi 0.13 cikin 100.
Wannan dai akasin abin da aka saba gani ne duk karshen shekara a Najeriya kasancewar lokaci ne na tashin farashin kaya saboda baukukuwan Kirsimeti da na Sabuwar Shekara.
Sai dai rahoton ya ce idan aka kwatanta faduwar 2022 din da ta 2021, alkaluman sun haura da kaso 6.30.
A bangaren kayan abinci irin su hatsi da burodi da kifi da sauransu kuma, NBS ta ce kari aka samu a farashinsu da kaso 23.75 cikin 100, wanda ya dara na Disambar bara da ya tsaya a kashi 17.37.
Wani manazarci kan harkokin kudi, Uche Uwaleke, ya bayyana wa Aminiya cewa saukowar farashin kayyakin ba zai rasa nasaba da sabbin tsare-tsaren Babban Bankin Najeriya (CBN) ba a kan kudi.
“Dalili daya za a ce ya haifar da hakan shi ne tasirin tsauraran manufofin kudi na CBN wanda nake hangen zai ci gaba da tasiri wajen faduwar farashin kayan a watanni masu zuwa, musamman saboda sake fasalin kudin da iyakance cirar tsabar kudi,” in ji shi.