✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bayan shekara 7: Shin Buhari ya cika alkawarin samar da tsaro?

Mazauna kauyukan Kaduna, Zamfara, Sakkwato da Katsina sun ce suna cikin ukuba.

Kafin zaben shekarar 2015, ’yan Najeriya da dama, musamman ’yan Arewa sun ta yi addu’ar ganin an kawar da gwamnatin Goodluck Jonathan daga mulki saboda matsalar rikicin Boko Haram a lokacin ta mamaye yankin.

Hakan ya sa Alhaji Muhammadu Buhari ya dauki alkawarin cire musu kitse a wuta idan ya zama Shugaban Kasa.

Jim kadan da hawan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari karagar mulki a shekarar 2015, sai ya ba da umarnin a mayar ofishin ba da umarni ga sojojin da ke fagen-daga daga Abuja zuwa Maiduguri, inda ake fama da yakin Boko Haram.

Ya kuma kara wa jami’an tsaro kudade, aka kuma sayo makamai da dama.

Ya dauki wadannan matakai ne don cika alkawarin da ya dauka na magance matsalar tsaro a kasar nan baki daya, kamar yadda ya sha alwashi a lokacin da yake yakin zabe.

An samu sauki sosai kan ta’asar Boko Haram, wanda hakan ya sa hankalin mutane ya fara kwantawa. Daga nan Boko Haram ta dare gida biyu a shekarar 2016, aka samu ISWAP daga Boko Haram.

A shekarar 2018 ce ’yan Boko Haram suka kai wani mummunan hari a garin Metele da ke Maiduguri, inda suka kwace sansanin sojoji makare da makamai, sannan suka kashe sojojin. Wannan hari yana daga cikin munanan hare-haren da aka taba kai wa dakarun Najeriya.

Sai dai daga baya an yi ta samun nasara a kan ’yan ta’addan, inda aka rika kwato garuruwan da a da suke hannunsu tare da fatattakarsu.

Sojojin sun samu nasarar kashe Muhammad Nur, sannan rikici a tsakanin ’yan Boko Haram da ISWAP ya ci Abubakar Shekau da Albarnawy, sai mayakan Boko Haram suka fara watsewa zuwa wasu yankuna, sannan daruruwansu suka mika wuya.

A daya bangaren kuma tun a wajajen shekarar 2002 a yankin Neja akwai ’yan kungiyar Ansaru da suka kafa garin Darul Islam, da aka fatattake su.

A yankin Zamfara kuma, Buharin Daji wani fitaccen dan bindiga ne da ya dade yana addabar mutanen Zamfara da satar shanu da kashe-kashe.

Wannan matsalar da ta faro daga Zamfara, ta fada Katsina ta kusan mamaye Arewa a yanzu.

A yankin Kudu maso Kudu, bayan shawo kan masu fasa bututun mai, sai tsagerun suka kafa haramtacciyar Kungiyar IPOB, mai rajin kafa kasar Biyafara a karkashin Nnamdi Kanu.

Sai kuma yankin Yarbawa da ke fama da matsalar rikicin kabilanci, wanda Sunday Igboho ya zo ya kara tsanantawa. Saboda ta’azzarar matsalolin tsaron ne aka matsa lamba har sai da Shugaban Kasa Buhari ya canja manyan hafsoshin sojin kasar, domin a samu sauyin da ake bukata.

Yanzu kusan saura watanni Shugaba Buhari ya kammala wa’adin mulkinsa na biyu, hakan ya sa Aminiya ta yi rahoto na musamman kan alkwarin samar da zaman lafiya da Shugaba Buhari ya yi da kuma halin da yankunan suke ciki.

Gwamnatin Tarayya na kokari kan matsalar tsaro – Lai Mohammed

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya ce Gwamnatin Tarayya tana kokari matuka wajen shawo kan matsalolin tsaro a kasar nan, inda ya ce “Ko kadan matsalar ba ta fi karfin gwamnati ba.

“Sojojinmu suna kokari sosai, kuma babu yadda za a ce aikin ya fi karfinsu,” kamar yadda ya bayyana a wata tattaunawarsa da tashar talabijin ta TBC a ranar Litinin da ta gabata.

Alhaji Lai Mohammed wanda ga alama yana mayar da martani ne kan kalaman tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo da ya ce matsalar tsaro ta fi karfin Buhari, ya ce ’yan ta’addan makiyan Najeriya ne, wanda hakan ya sa ya yi kira ga ’yan Najeriya su ma su ki su.

Ya ce yaki da ta’addancin irin wanda Najeriya ke fama da shi, ba kamar yakin da aka saba ba ne.

Game da harin jirgin kasa da aka kai a Kaduna, Ministan ya ce Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin ganin hakan bai sake faruwa ba.

Ya ce, daya daga cikin matakan da Shugaba Buhari ya dauka shi ne bayar da umarnin a gaggauta sanya na’urar bibiyar layin dogon.

“Ba layin dogon Abuja zuwa Kaduna kadai ba, har da na hanyar Legas zuwa Abuja da Warri zuwa Itakpe/Ajaokuta, duk za a sa musu na’urar.

“Za a yi haka ne domin a koyaushe ya kasance ana ganin abubuwan da suke faruwa a layin dogon daga dakin kula da ke tashar, kamar wadanda suke da burin batawa ko kai hari ga hanyar dogon.

“Sojoji sun yi kokarin dakile su a wasu lokutan a baya, amma dama haka ’yan ta’adda suke, za su yi ta neman wasu hanyoyin ne don nuna gazawar sojojin.

“Kada mu mance, duk da cewa an samun matsalar harin jirgin kasa, lallai sojojinmu suna kokari matuka wajen yaki da ta’addanci,” inji shi.

Yankin Arewa maso Yamma

A Jihar Kaduna, yanzu haka akwai kauyuku da yawa a kananan hukumomin Giwada Chikun da Birnin Gwari da Kaura da Igabi da Kajuru da suka watse saboda yawan hare-haren ’yan ta’addan.

A wani rahoton shekarar 2021 da Kwamishinan Tsaro da Al’amurar Cikin Gida Samuel Aruwan ya gabatar wa a Gwamnan Jihar ya ce akalla mutum 1,192 aka kashe a jihar.

Game da satar mutane, rahoton ya nuna an sace akalla mutum 3,348 a jihar inda yankin Kaduna ta Tsakiya ke gaba da mutum 2,771.

Kwanan nan ’yan bindiga suka hallaka sama da mutum 50 a kauyuka tara a Karamar Hukumar Giwa. Sannan bayan kwana biyu suka sake kashe mutum 15 a Gundumar Yakawada.

Harin da ya fi daukar hankali shi ne na jirgin kasa a hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar 28 ga watan Maris inda aka kashe akalla mutum 9 aka raunata 26, sannan har yanzu ba a san yawan mutanen da aka sace ba.

Wannan hari ya girgiza al’ummar jihar da kasa baki daya domin ita ce hanya daya tilo da mutane ke ganin ta fi saukin bi saboda kauce wa ’yan ta’addan da suka addabar matafiya a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Muna cikin ukuba

Mazauna kauyukan Kaduna Malam Muhammadu Umaru mazaunin kauyen Udawa da ke Karamar Hukumar Chikun ya ce a yanzu al’amura sun fi muni a wannan mulki.

“A wancan gwamnati bam ne ke tashi sai kuma wuraren binciken ababen hawa a kanhanya da muka rika kokawa da su. Amma a yanzu al’amuran sun canza kauyuka ake zuwa ana sace mutane a kashe na kashewa.

“A gaskiya wannan gwamnati ba za ta iya kare mutane ba,” inji shi.

Ya ce ’yan ta’addan sukan tunkari sojoji a daji amma idan suka hango ’yan sintiri sai su gudu. Wannan ya sa suke tunanin abin akwai siyasa a ciki.

Sai ya bukaci jama’a su koma ga Allah a yi ta addu’a ko za a samu saukin bala’in. Wani mazaunin Giwa mai suna Ridwanu ya ce hakika Karamar Hukumar Giwa na neman zama Sambisa saboda kashe-kashen da suke faruwa a kauyukansu.

“Yanzu Giwa muna cikin tashin hankali saboda hare -haren ’yan bindiga da kuma kisan mutane da ake yi.

“Abin damuwa shi ne a cikin kwana hudu kawai an kashe kusan mutum 100 a Giwa kadai,” inji shi.

Daya daga cikin dattawan Unguwar Barde da ke kan titin Kaduna zuwa Abuja ya ce, “Muna cikin tashin hankali domin ban taba ganin irin wannan abin ba a ce mutumin karkara za a daure a ce sai ya biya kudin fansar kansa ko a hallaka shi. Ba ka da abinci ballantana kudi tunda an hana ku noma.

“Wannnan ai masifa ce,” inji shi.

Kungiyar Ci-gaban Masarautar Birnin Gwari a wata sanarwa da ta fitar a makon jiya dauke da sa hannun Shugabanta Is’hak Usman Kasai, ta ce a yanzu ’yan bindiga ke juya akalar wasu kauyuka inda suke karbar haraji a hannun mutanen da suke neman kariyarsu sannan idan suka ga dama su kai hari kauyukan tare da kashe mutane duk da sun karbe masu kudade.

“Muna kira ga shugabanni su fahimci cewa ba a siyasa idan babu zama lafiya. Akwai bukatar daukar matakai domin kare Birnin Gwari tun kafin garin ya watse. Saboda a yanzu gabashinsa duk suna karkashin ’yan ta’adda ne musamman yankin Tabanni da Dogon Dawa da sauran kauyuka,” inji shi.

Babu zaman lafiya a yankinmu – Mutanen Sakkwato da Zamfara

Jihar Zamfara na cikin jihohin da suka fara fama da matsalar ’yan bindiga, inda ake yawan samun kwan-gaba-kwan-baya wajen samun sauki da ta’azzarar lamarin.

Dokta Yakubu Aliyu Gobir malami a Jami’ar Usman Dan Fodiyo, ya ce harkar tsaro a yankinsu ba su gani a kasa ba kan alkawarin Shugaba Buhari na samar da zaman lafiya.

Ya ce, “Ranar Litinin da ta gabata ma a garin Malam da ke Karamar Hukumar Sabon Birni mutum hudu aka yi garkuwa da su.

“Yakin da ake yi da maharan ana nuna ba da gaske ake yi ba domin kamata ya yi a bi mutanen har dabarsu, ba sai an jira sun fito sun je sun yi garkuwa da mutane ba.

“Har wani shiri aka tashi na daukar maharba su shiga dajin Rabah har zuwa Gundumi tare da jami’an tsaro amma aka fasa, mun san da an yi haka da yanzu an kawar da ’yan bindigar nan, wannan ya sa da yawanmu ke ganin kamar wadansu ’yan siyasa da manyan sojoji ba su son a kare wannan matsalar ta tsaro.

“Su ’yan siyasa domin siyasarsu su kuma sojoji domin abin da suke samu, su kuma kananan sojoji gudun kada su shiga a kashe su kuma ba wani tanadi da aka yi musu, wadannan abubuwa ne suke sa ba a gani a kasa ba a harkar tsaro duk da alkawarin Shugaba Buhari.”

Alhaji Nasiru Suleiman Goronyo yana ganin gwamnati ta yi kokari sosai, sai dai ya ce matsalar ita ce, “Masu kai wa ’yan bindiga bayani.

“Ko sojoji kadan ne aka kawo maharan suna jin tsoro, amma ba za su kai hari ba sai sojoji sun bar wurin. Hakan ke nuna akwai masu ba su bayani kuma su ne matsalar.

“Da za a samu hanyar kawar da su za a gani a kasa kamar yadda ake so,” inji Goronyo.

Alhaji Bashir Altine Guyawa Isa ya ce ba su ga wani abu na inganta tsaro ba don jami’an tsaro ba su da makamin kwarai. Ya ce, “A kullum ba wani mataki na inganta tsaro an kashe sojoji da dama a Goronyo da ’Yarbulutu da Sabon Birni da Gundumi.

Kullum ayyukkansu na kassara sojoji ne, duk masu ta’addanci a lungunanmu ba wanda aka kawar. “Ba mu ga wata hanya da aka bi don magance matsalar tsaro ba, in har gwamnati ta yi kokari ba a Sakkwato ba ne, ’yan bindiga irin su Dogo Gide da Baleri da Turji ba a samu galaba a kansu ba duk abin da ka gani addu’a ce ba wai don ana fada da su ba.

“Maganar gani a kasa abu ne mai sauki in gwamnati ta daukinauyin kula da matasa a ba su abin yi, ba wai irin wannan kudin da ake kashewa ana bayarwa na kyauta ba, a samar da aikin yi ba wannan aikin rufe zanen ’yan bori ba”, inji shi.

Malam Abdul Muhammad Gumi a Jihar Zamfara ya ce su ba su gani a kasa ba, domin abin da gwamnati ke fadi daban abin da ake aiwatarwa a yankunansu daban.

“Harkar tsaro ta tabarbare kuma aba ce da ya kamata gwamnati ta tashi tsaye a kanta domin muna cikin ukuba da tashin hankali har da mutanenmu na yankin Anka da Maru,” inji shi.

Malam Muhammad Maniru ya ce lamarin tsaro a Zamfara abu ne kamar layin sadarwa, inda yau ka ji an samu sauki, gobe akasin haka za ka ji.

Ya ce, “Amma magana ta fahimta ba wani zancen an gani a kasa sai dai a dauki matakin kawo gyara, domin mutanen Zamfara sun sha bakar wahala.”

Za mu dauko sojojin haya daga waje – El-Rufa’i

Da yake jawabi bayan harin jirgin kasa, Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce idan Gwamnatin Tarayya ta kasa magance matsalar za su dauko sojojin haya domin su taimaka wurin fattatakar ’yan ta’addan.

Sai dai batun na Gwamnan bai samu karbuwa ba a wajen wadansu, inda Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta nuna rashin amincewarta.

Shugaban Kungiyar, Rabaran John Joseph Hayab tambaya ya yi wasu rin sojojin haya Gwamnan yake nufi.

Ya ce in da wani dan kasa ne ya yi wannan magana za a nuna ya yi laifi ko a ce ya raina Shugaban Kasa wanda shi ne kwamnadan hafsosin kasar nan.

“Don haka muke kira ga Gwamnatin Tarayya ta ja masa kunne tun kafin ya jefa jihar da kasar cikin matsala musamman a yanzu da ake tunkarar zaben 2023,” inji shi.

Ya ce kungiyar za ta ci gaba da yi wa kasa da jiha addu’ar samun zama lafiya a kan wannan matsala ta tsaro da ake fuskanta.

Ita ma Kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF) ta nuna rashin amincewa da dauko sojojin haya daga waje, inda ta yi kira ga gwamnati ta dauki matakan da suka dace wajen kare rayukan al’umma.

Jihar Katsina

A Jihar Katsina, kananan hukumomi tara ne daga cikin 34 suke fuskantar wannan matsala. Malam Lawal Jibiya ya ce, “Abu na baya-bayan nan da ya faru a garin Shimfida a yankin Jibiya shi ne, bayan kwashe sojojin da ke garin da aka yi ba wata sanarwa ko dalili, sai mutanen garin suka rika shigowa Jibiya saboda tsoron abin da zai biyo baya.

Yanzu maganar da nake yi da kai babu kowa a cikin garin duk suna nan Jibiya. Batun tafiya da mutane cikin daji ba a ma magana. Ta ina za a ce an samu nasara a batun tsaro?”

Shi kuwa Malam Saminu da ke yankin Batsari cewa ya yi, “Kwanan nan ’yan ta’addan suka ce ga su nan zuwa garin Batsari daukar fansa a kan an kashe masu mutane, kuma har zuwa yanzu babu wani kwakkwaran mataki da muka ji an dauka a kan wannan barazanar.

“Yau shiga wasu yankuna irin su Kandawa da Dankar da Nahuta da Tsauwa da sauransu ya yi wuya.

“Karshe har kusa da birnin Katsina, can garin Barawa da Jino ba su tsira ba, duka kuma kilomita nawa ne shiga cikin garin Katsina?”

Mutanen da Aminiya ta zanta da su a yankunan da matsalar tsaron ta shafa, babu inda suka nuna an samu nasara a kan batun tsaron sai dai abin da ba a rasa ba, musamman a yankunan da ke kan iyaka da dajin Zamfara da dajin Rugu ko na Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.

‘An samu sauki a Arewa maso Gabas’

A yankin Arewa maso Gabas da Gwamnatin Buhari ta samu da matsalar Boko Haram, wani matashi a garin Gashuwa da ke Karamar Hukumar Bade a Jihar Yobe, Malam Adam A. Adam, ya ce, “Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya cika mana alkawarin da ya dauka na cewa da taimakon Allah zai magance mana rikita-rikitar da muke fama da ita ta Boko Haram.

“Yanzu sai dai mu ce alhamdulillah, kwalliya ta biya kudin sabulu domin rabonmu da mu ji an ce an samu tashin bam a masallatai ko wuraren taruwar jama’a da kan halaka rayukan jama’a da jin munanan raunukan har mun manta.

“Don haka mu al’ummar Jihar Yobe mun gamsu kan ingantuwar tsaro a dukan bangarorin jiharmu,” inji shi.

Shi ma Malam Saleh Bakwaro nuna gamsuwa ya yi game da yadda harkokin tsaro suka inganta a jihohin Yobe da Borno sakamakon jajircewar Shugaba Muhammadu Buhari.

Ya ce duk da cewa har yanzu a Jihar Borno akwai wuraren da suke hannun Boko Haram da ISWAP, amma lallai sun ga canji wajen samun saukin matsalar tsaro a yankin.

Kudu maso Gabas

Aminiya ta tattauna da wadansu mazauna jihohin Kudu maso Gabas kan matsalar tsaro a yankin inda suka bayyana yadda girmanta take.

Maganar kafa kasar Biyafara da kuma dokar zaman-gida a kowace Litinin da ’yan Kungiyar IPOB suka tilasta wa mazauna yankin da ’yan kasuwa masu shiga da fita ce matsalar da ta fi ci wa yankin tuwo a kwarya.

Malam Muhammad Aminu, mazaunin Kudu maso Gabas, ya ce, “Matsalar tsaro sai dai mu ce alhamdulillah saboda duk halin da mutum yake ciki dole ne ya gode wa Allah. Amma ana cikin fargaba.

“Ka ga yanzu wata 9 ke nan babu cikakken zaman lafiya saboda dokar zaman gida dole da ’yan Kungiyar IPOB suka tilasta wa mutane,” inji shi.

Malam Aminu ya ce, “A waccan gwamnatin ma akwai matsalar tsaro amma ba ta kai ta wannan gwamnati ba.

“Masu fafutikar kafa kasar Biyafara na yawo kasuwanni da wuraren da ’yan Arewa suke kasuwanci, inda ya ce ana yi musu kisan dauki dai-dai tare da kwace masu dukiya.

“Yanzu ’yan Arewa mazauna Kudu maso Gabas da aka kashe sun haura 170.

“Ko a wannan mako ma sai da aka kashe mutum uku a Orlu da ke iyaka da Jihar Imo,” inji shi.

Muhammadu K. Salisu ya ce, “Matsalolin da muke fuskanta ba za su wuce na kabilanci da nuna mana bangaranci ba. Kuma ana nuna mana bambancin addini ana kawo mana hari.”

Shi kuma Alhaji Muhammad Sani cewa ya yi, “Hakika matsalar tsaro ta lalace a Kudu da Najeriya. Mu mazauna Jihar Imo da wasu sassan Kudu maso Gabas ba mu da kwanciyar hankali,” inji shi.

Tsaro a Legas da jihohin Kudu maso Yamma

A jihohin Kudu maso Yamma al’amuran tsaro sun yi rauni tun bayan zanga-zangar #EndSARS, inda hakan ya sa ake samun karancin ’yan sanda a manyan hanyoyi musamman daga yamma zuwa dare kuma hakan na bai wa batagari damar cin karensu babu babbaka, suna tare masu ababen hawa su yi masu kwace, sai kuma matasa ’yan kungiyar asiri.

Alhaji Ado Shu’aibu Dansudu, Shugaban Gamayyar Kungiyoyin ’Yan Arewa tare da tuntubar juna, ya ce tsaron da ake samu a Jihar Legas da daukacin jihohin Kudu maso Yamma jajircewar gwamnonin yankin shida ne, wadanda a lokacin da suka fara fuskantar matsalar tsaro suka kau da bambance-bambance siyasa da na addini suka hada kai suka tunkari matsalar.

“Wannan hadin kai nasu ne ya haifar da kungiyar sa-kai ta tsaro da suka samar bai-daya a jihohin Kudu maso Yamma, wato Amotekun, wacce sun kafa ta ce don kawo karshen matsalolin da suke da nasaba da garkuwa da mutane da rikicin Fulani makiyaya da manoma.Kuma za a iya cewa wannan yunkuri kwalliya ta biya kudin sabulu,” inji shi.

Ya ce da a Arewa gwamnoni za su hada kai su yi koyi da takwarorinsu na Kudu za a samu saukin tashin-tashanar da ke addabar yankin.

’Yan ta’adda na neman tarwatsa tattalin arzikin Kaduna- Masana

Wadansu masana harkokin tsaro sun nuna damuwarsu a kan hare-haren ’yan ta’adda a Jihar Kaduna inda suka ce idan ba a dakile ba zai shafi tattalin arziki mutane da na jihar.

Wani masanin tsaro a jihar, Awwal Abdullahi Aliyu ya ce hare-haren na neman mayar da Jihar Kaduna abar tsoro. “Mutane za su rika jin tsoron zuwa saboda ana ganin jihar a matsayin wuri mai hadari saboda garkuwa da mutane,” inji shi.

A nasa bayanin kan matakin da wasu kamfanonin jiragen sama suka dauka na daina zuwa Jihar Kaduna, Farfesa Seth Akutson na Jami’ar Jihar Kaduna, a Sashen Tattalin Arziki ya ce tattalin arziki jihar na iya shiga matsala.

“A matsayin daya daga cikin manyan jihohi masu karfin tattalin arziki bayan jihohin Legas da Kano da ke da mutum sama da miliyan 10.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi gine-gine da manyan shagunan zamani, amma idan babu tsaro duk wadannan abubuwa ba wanda zai yi sha’awar zuwa,” inji shi.