A karon farko cikin kusan shekaru 15, ana shirin kulla cinikayyar dan wasa kai tsaye tsakanin manyan abokan hamayya a gasar La Liga, wato Real Madrid da Barcelona.
Rabon da a ga irin wannan sauyin sheka dai tun shekara ta 2007, lokacin da Javier Saviola ya koma Real Madrid daga Barcelona.
- Ina dan wasan da ya zura kwallon da Najeriya ta lashe AFCON 2013, Sunday Mba, yake?
- AFCON: Yadda alkalin wasa ya hura tashi lokaci bai yi ba
A halin yanzu kuma dan wasan tsakiyar Real Madrid Isco Alarcon ke shirin sauyin shekar zuwa Camp Nou.
Gidan Rediyon Faransa ya ruwaito cewa, tuni dai aka tsegunta cewar har ma Isco ya gana da kocin Barcelona Xavi Hernandez.
Dan wasan mai shekaru 29 a yanzu shi ne na biyar a matakin muhimmanci tsakanin ‘yan wasan tsakiya na Real Madrid da suka hada da Toni Kroos, Luka Modric, Federico Valverde, da kuma sabon dan wasa Eduardo Camavinga.
Wannan dai ya biyo bayan yadda a kakar wasa ta bana, wasanni 9 kawai Isco ya buga a karkashin kocinsa Carlo Ancelotti, wanda ga dukkanin alamu dan wasan baya cikin tsarinsa.
A cikin watan Yunin shekarar nan yarjejeniyar Isco za ta kare da Real Madrid, lokacin da ake sa ran zai koma Barcelona.
Wasu majiyoyi a Sifaniya sun ruwaito cewar, dama can Isco Alcaron magoyin bayan Barcelona ne na bugawa a jarida, tun ma kafin ya kulla yarjejeniya da manyan abokan hamayyarsu a shekarar 2013.