Hukumar Kula da Matasa Masu yi wa Kasa Hidima (NYSC) ta fara ba da horo ga matasa masu yi wa kasa hidima su 1,161 a sansanin horar da malamai na ATC da ke Jihar Borno.
Kimanin shekaru 12 ke nan sansanin ya shafe a rufe sakamakon ta’addancin Boko Haram.
- Kwale-kwale ya kife da mutum 300 a tsakiyar kogin Kwango
- Sojoji sun kama jirgin ruwa makare da lita 350,000 na man dizel din sata
Fara horarwar wanda aka shirya yi a ranar Juma’a mai zuwa a Maiduguri, zai gudana ne a sansanin mai daukar mutane 3,000.
Ko’odinetan hukumar ta na jihar, Mohammed Adamu, ya ce, “Sojoji, ’yan sanda da sauran jami’an tsaro sun tabbatar mana da tsaron jami’anmu, da jami’an wayar da kan jama’a da kuma jami’an hukumar da ke wannan sansani da aka gyara.”
Ya yi nuni da cewa, an dawo da shirin ne bayan shekaru 12 da Boko Haram ta fara ta’addanci a jihar kamar yadda aka ambata a baya.
Dangane da dabarun da sansanin yake da shi, ya ce: “Sansanin ATC na gwamnatin jihar da aka gyara yana tsakiyar ofisoshin hukumomin tsaro da ke kan titin filin jirgin saman kasa da kasa na Janar Muhammadu Buhari a Maiduguri.”
Don haka ya kawar da duk wata fargabar da iyaye da masu kula da su ke da ita ta kare lafiyar ’ya’yansu a lokacin da za su karbi horo na mako uku.
Ya kara da cewa mazauna Maiduguri da suka hada da Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn El-Kanemi, sun cika makil da farin ciki kan yadda za a dawo da horar da matasan a Jihar.
Da yake duba sansanin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Mohammed Yusuf, ya ce, “Makasudin ziyararmu ita ce duba yanayin tsaro a yankin, tare da sanin hakikanin yadda aka tura jami’an tsaro.”
Don haka, Kwamishinan ya ba da tabbacin tura isassun jami’an ’yan sanda a wuraren shiga da fita sansanin, gami da muhimman wurare na tsaro.