Bayan shekara goma Gwamnatin Jihar Yobe ta dage haramcin amfani da babura masu kafa biyu a duk ilahirin Kananan Hukumomi 10 da ke Kudu da Arewacin Jihar.
Gwamnan Jihar Mai Mala Buni ne ya sanar da hakan a Fadar Sarkin Nguru, inda ya ziyarta domin jajanta wa al’ummar yankin dangane da ibtila’in gobara da ya auku a Babban Kasuwar Nguru.
- Kofin Afirka: ’Yan Arewa da ke cikin tawagar ’yan wasan Najeriya
- Na sanar da Buhari kudirina na neman takarar shugaban kasa —Tinubu
Gwamnan ya sanar cewa a yanzu mazauna jihar suna da ’yancin amfani da babura domin saukaka musu sufurin zuwa gonaki da sauran wuraren da suka bukata.
Ya jaddada cewa wannan sabon matakin na zuwa ne a sakamakon yanayi na ci gaban da aka samu a fannin tsaro a yankunan.
Ana iya tuna cewa, tun a shekarar 2012 da ta gabata ce Gwamnatin Jihar Yobe ta haramta amfani da babura masu kafa biyu a yayin da rikicin Boko Haram ya tsananta.
Daga cikin Kananan Hukumomin da aka sahalewa amfani da baburan a yanzu sun hada da Bade, Nguru, Karasuwa, Yusufari, Machina, Jakusko, Fune, Fika, Nangere da kuma Potiskum.